Tafarkin sunnah


Xan Shi’ah ya yi Hujja da wannan Aya



Yüklə 2,75 Mb.
səhifə44/51
tarix28.10.2017
ölçüsü2,75 Mb.
#17506
1   ...   40   41   42   43   44   45   46   47   ...   51

6.3.2 Xan Shi’ah ya yi Hujja da wannan Aya:

ﭽ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬ ﭭ ﭼ الحاقة: ١٢

Xan Shi’ar ya ce: Kuma saboda Ali Raliyallahu Anhu ne ayar da ke cewa: Don mu sanya maku ita ta zamo faxakarwa. Kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye ta (60:12) ta sauka.

Martaninmu a nan shi ne: Wannan magana qarya ce bisa haxuwar malamai. Abin da gaba da bayan ayar ke tabbatarwa shi ne, Allah Subhanahu Wa Ta’ala ba ya nufin wani kevantaccen kunne na wani kevantaccen mutum da wannan aiki na kiyayewa. Duk wani kunne ko na kowa ne, yana cikin wannan manufa matuqar dai yana iya kiyaye wa’azin Ubangiji.


6.4 Kaifin Basirar Ali

Xan Shi’ar ya ce: kuma Ali Raliyallahu Anhu ya kasance mai kaifin basira da tsananin kwaxayin neman ilimi. Ya kuma yi tarayya da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a matsayinsa na mafi kamala a cikin mutane, ta yadda dare da rana ba su raba su. Wannan kuma tun lokacin da Aliyu yake yaro kowane har lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya rasu.

Martaninmu a nan shi ne: Ta wace hanya ‘yan Shi’ah suka sami labarin cewa Ali Raliyallahu Anhu ya fi Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma kaifin basira da kwaxayin neman ilimi, da kasancewar abin da ya fa’idanta da shi daga wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fi nasu?

Abin da ya inganta daga Buhari da Muslimu shi ne, cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Haqiqa a cikin al’ummomin da suka gabace ku akwai waxanda ake sanar da su. Da xaya zai kasance a cikin al’ummata to, Umar ne”.

Ko shakka babu taren da Abubakar ya yi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin musulunci ko rabinta Aliyu bai yi ba, kai babu ma wani mahaluki da ya yi irinta. Irin damar da Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma suka samu ta haxuwa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kowane lokaci, Ali Raliyallahu Anhu bai same ta ba. Su ne mutanen da Annabi ke tattaunawa da su a kan duk wani abu da ya shafi musulmi. Kuma mafi yawan matsalolin da Umar da Ali suka qara wa juna ilimi a cikinsu, ijtihadin Umar ne kan cira tuta. Kamar matsalar wadda mijinta ya rasu ya bari da ciki.
6.4.1 Malam Zurqe Bai ko San Hadisi ba

Xan Shi’ar ya ce wai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Karatu a lokacin qurciya kamar zane ne a kan dutse. Wai saboda haka, inji xan Shi’ar, Ilimin Ali Raliyallahu Anhu ya fi na duk wanda ba shi ba, don ya yi shi tun yana da qurciya.


Martani:

Wannan magana na tabbatar da kasancewar xan Shi’ar nan riqaqqen jahili a fagen ilimin hadisi. Wannan zance da ya ce Annabi ya yi ba hadisi ne ba, don Annabi bai faxe shi ba. Salon magana ce kawai da ta yawaita a tsakanin musulmi.

Babban abin da ke tabbatar da haka, shi ne, Sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na da haqoransu talatin talatin suka karanci rukunnan imani da Qur’ani, suka koyi sunnoni, duk a cikin taimakon Allah. Shi kuma sayyidina Ali kansa ko kafin Alqur’ani ya qare sauka, shekarunsa sun cika talatin cif. Ka ga kenan, sashen Alqur’ani ne ya hardace a quruciya. Sauran kuma da girmansa ne ya hardace su. Ballantana ma dai babu tabbas game da kasancewarsa ya hardace Alqur’ani dukkansa. Domin kan malamai bai haxu a kan haka ba.

To, ba Sahabbai ba ma, Annabawan Allah, waxanda su ne mafiya ilimi a cikin halittun Allah, babu wanda Allah ya aiko a cikinsu yana xan qasa da shekaru arba’in. Hana rantsuwa a wannan magana shi ne Annabi Isah. Kuma ka ga Abu Hurairata, duk da kasancewarsa dattijo, amma a cikin shekara ukku da ‘yan watanni ya hardace ilimi mai yawa a makarantar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Haxuwar Abubakar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kuwa ta fi ta sauran Sahabbai.


Sai cewar da xan Shi’ar ya yi, wai, daga wajen Ali mutane suka san karatu. Qarya ce. Don mutanen garinsa Kufa sun daxe da yin karatu mai zurfi ta hannun Ibnu Mas’ud da wasu malamai kafin Ali Raliyallahu Anhu ya saka qafarsa a birninsu.

In ko yana tunanin kafa hujja da cewa; Baban Abdurrahman As-Sulami daga wurin Ali ne ya xauki qira’a. Sai mu ce masa, bita ce kawai ya yi. Domin kafin zuwan sayyidina Ali Raliyallahu Anhu garin Kufa Baban Abdurrahman alaramma ne, mai riqaqqar harda.


6.4.2 Wai Ali ne ya Qaga Ilimin Nahawu!

Xan Shi’ar ya ce: Shi kuwa ilimin Nahawu Aliyu Raliyallahu Anhu ne ya shimfixa shi, don shi ne ya ce wa abul Aswad: Kowace irin magana ba ta wuce abu uku, da suka haxa da: Suna, da Aiki da Harafi. Daga nan kuma ya naqalta masa fannonan li’irabi.


Martani:

Abin da za mu ce a nan: Shi ilimin Nahawu ba ya cikin ilimin Annabta. Qago shi aka yi. Kuma wani salo ne na kare mutuncin qa’idojin harshe, da sauqaqe wa al’umma gane Alqur’ani. A zamanin halifofi uku na farko, ba a buqaci yin sa ba, don babu wanda ke dolge a harshen Larabci. Sai a lokacin da Ali Raliyallahu Anhu ya koma birnin Kufa da zama ne inda ajamawa su ke. Nan ne aka riwaito sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ya yi waccan magana ga Abul Aswad.

Ka ga sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ya yi wannan aiki saboda wata lalura, kamar yadda aka samu cewa, wasu a bayan wucewarsa, sun tsago salon rubuta baqaqe da xigagga da wasulla, da alamomin jan baqi da konkoma shi da makamantansu, duk a kan wata lalura. Bayan haka ne malamai a Kufa da Basra suka kyautata tace ilimin Nahu da faxaxa shi. Malam Khalil kuma daga bisani ya tsago ilimin Aruli.

To, ina abin da ke nuna Ali halifa ne a cikin wannan batu?


6.4.3 Fiqihun Ali

Xan Shi’ar ya ce: Ali shi ne madogarar malaman fiqihu a karatunsu.


Martani:

Wannan magana qarya ce kamar ‘yan’uwanta da muka saba ji. Babu dai wani malami daga cikin malaman fiqihun Sunna guda huxu da aka sani ko wani ba su ba, wanda ke dogara ga Ali Raliyallahu Anhu a fiqihunsu.


6.5 Jaruntakar Ali ba Dalili Ce a Nan ba

Xan Shi’ar ya ce: Sayyidina Ali ya kasance mafi jarunta a cikin mutane. Da kaifin takobinsa ne kuma qa’idojin musulunci suka sami gindin zama, kuma rakunnan musulunci suka tsaya da qafafunsu. Ba a tava cin sa da yaqi ba, kuma bai tava bugun wani abu da takobinsa ba face ya gama da shi. Da yawa kuma Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ya yaye baqin ciki daga fuskar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Wai kuma sayyidina Ali Raliyallahu Anhu bai tava gudu daga fagen fama ba kamar yadda wasunsu suka yi.

Shi ne kuma ya bai wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kariya ta hanyar kwantawa a kan shimfixarsa da yin lulluvi da bargonsa, a ranar da mushrikkai suka haxa kai a kan kashe shi. Da aka yi haka sai suka zaci wancan da ke kwance kuma a lulluve Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne, alhali kuwa Ali ne, sai suka yi dako-dako da makamai suna jiran alfijir ya keto su far masa, su yi masa bugun a kawo wuqa, jininsa ya tafi bakin banza, tunda banu Hashim ba za su iya yaqi da gaba xayan qabilun Larabawa ba, waxanda suka haxa guiwa, suka kashe shi. A haka, sai kowa ya tsira daga cikin qabilun. Wannan jaruntaka ta sayyidina Ali ce sanadiyyar kuvutar jinin Manzon Allah daga zuba a banza. A qarshe aka samu tsira, har gurin kira zuwa ga tafarkin Allah ya tabbata.

Da gari ya waye mushrikan suka yi azmar xaixaita shi, sai ya kai masu matsanancin farmaki. Ko da dai suka ga ashe Ali ne, sai kowanensu ya ranta cikin na kare; suka watse, mugun nufi da mummunar dabararsu, suka tsaya nan.


Martani:

Amsarmu ga wannan ita ce: Ko shakka babu sayyidina Ali Raliyallahu Anhu na xaya daga cikin jarumawan Sahabbai waxanda kuma qoqari da yajinsu ya taimaki musulunci. Yana kuma daga cikin ‘yan sahun gaba daga cikin Muhajiruna da Ansaru, haka kuma sahun magabata daga cikin waxanda suka yi imani da Allah da ranar qarshe ba ya cika sai da shi a ciki. Gaskiya ne Ali ya kashe adadi mai yawa na kafirai da takobinsa.

Amma duk da haka, Ali bai kevanta da waxannan siffofi ba. Akwai Sahabbai da dama da suke kafaxa-da-kafaxa da shi a wannan fage. Wannan ba ya sa ya zama mafi daraja a kan Sahabbai idan ana zancen jihadi balle a kan halifofi. Balle kuma hakan ya zama dalilin zamansa shugaba a kan kowa.

Idan muka xauki wannan magana tasa dalla–dalla; muka fara da cewar da ya yi: Ali shi ne mafi jaruntaka a cikin mutane, za mu ga hakan ba gaskiya ba ne. Tabbatattar magana, ita ce Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ne jarumi na qarshe a cikin mutane. Kamar yadda Buhari da Muslimu suka riwaito daga Anas, wanda ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kasance mutum mafi kyawo da inganci da jaruntaka a cikin mutane. Watarana firgita ta kama mutanen Madina, saboda wata qara da suk ji, sai suka tasar ma inda ta fito baki xaya. Kafin su kai, sai suka haxu da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yana tafe sukane a kan wani doki na Abu Xalhata da takobi rataye a wuyansa yana ce masu, kar ku ji tsoron komai. Buhari ya ce: Annabi ya je wurin da abin ya faru tun kafin su fito.

Ya kuma zo a cikin Musnad daga Ali Raliyallahu Anhu ya ce: Mun kasance a duk lokacin da tsanani ya kai mana mashafar turare mukan lave ne a bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Shi ne wanda ya fi mu zama kusa da abokin gaba. To, ka ga wannan magana gaskiya ce. Amma a cikin Sahabbai akwai waxanda suka kashe fiye da adadin da Annabi ya kashe na kafirai da hannunsa.

To, ko bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, Abubakar Raliyallahu Anhu ma ya fi Ali Raliyallahu Anhu jaruntaka. Domin shi ke take sawun Manzon Allah a wannan fage. Abubakar ne kuma ya ceto musulmi daga kiximewar da suka yi ranar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya rasu. Wannan masifa ita ce fitina mafi girma da nauyi a wajen musulmi. Kaxan ne daga cikinsu wanda hankalinsa bai fita daga jikinsa ba, hantarsa ta kaxa, ya ruxe, ya kaxu kamar majaujawa saboda wannan gigita a kan rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Wasu daga cikinsu na yunqurin cewa, ai ba ta yiwuwa Manzon Allah ya rasu. A daidai lokacin, wasu jiki suka yanke, suka faxi zaune, wasu kuma sun ximauce; ba su san abin da ke kaiwa yana komowa ba. Wasu kuma sai kuka suke faman rusawa kamar dai watarana ce qarama daga cikin ranakkun Alqiyama suka wayi gari a cikinta.

Nan take sai Abubakar siddiqu ya zabura, zuciyarsa cike da kuzari da saxaukantaka, ba tsoro ba fargaba, fuskarsa na nuna haquri da yaqini, ya tabbatar masu da cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama dai ya riga mu gidan gaskiya. Allah ya zavar masa abin da ke can wurinsa. A nan ne ya saki shahararrar huxubar nan tasa, bakandamiya, wadda a cikinta yake cewa: “Ya ku mutane! Duk wanda ke bautar Muhammadu to, ya sani Muhammadu kam ya kwanta dama. Wanda kuwa Allah ne yake bauta wa to, ya sani Allah rayayye ne, kuma babu ranar da zai mutu”.

Jaruntakar duk da ake buqata ga wanda ya kamata a ce shi ne shugaba bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta tabbata ga Abubakar. Sannan Umar ne zai biyo bayansa.

Idan kuma muka koma ga zancen adadin kafiran da Ali ya kashe. Za mu tarar cewa, a tarihin yaqoqan musulunci an samu Sahabban da suka kashe fiye da abin da Ali Raliyallahu Anhu ya kashe daga cikin kafirai. Idan kuwa yawan adadin abin da mutum ya kashe na kafirai ne ke tabbatar da fifikonsa a jaruntaka. Kenan waxancan Sahabbai sun yi wa Ali Raliyallahu Anhu fintinkau a wannan fage.

Xauki misalin Bara’u xan Malik, xan’uwan Anas, wanda ya kashe qato xari ta hanyar gani-ga-ka. Wannan ban da waxanda ya kashe a cikin sahu, ko waxanda yake da hannu a cikin kashe su. To, qarewa da qarau ma shi Khalidu xan Walidu sanin adadin kafiran da ya aika lahira sai masanin gaibi, shi ne, Allah, amma dai ba mutum ba. Kansakalin takobi tara ne suka karye a hannunsa wajen yaqin Mu’uta kawai. ko shakka babu Khalidu ya kashe ninkin ba ninkin abin da Aliyu ya kashe a fagen fama.

Sai kuma cewar da ya yi a qarqashin inuwar kaifin takobin Ali ne ginshiqan musulunci suka sami zama da gindinsu, rukunansa suka tsaya a kan qafafunsu. Wannan qarya ce bayyananna ga duk wanda ya san tarihin musulunci. Amma dai babu mai musun cewa, lalle takobin Ali ya taka muhimmiyar rawa a cikin rawar da takubban wasu Sahabbai da dama suka taka wajen sama wa musulunici mazauni a bisa doron qasa. Akwai kuma waxansu nasarori da musulunci ya samu waxanda takobin na Aliyu Raliyallahu Anhu ba ya da wani dogon tasiri a ciki. Kuma waxannan nasarori a tarihin musulunci su ne mafi yawa, kamar dai yaqin Badar. Takobin Ali Raliyallahu Anhu xaya ne kawai daga cikin takubba masu xinbin yawa da aka yi yaqin da su.

Cewar kuma da xan Shi’ar ya yi, ba a tava nasara a kan Ali a wurin yaqi ba. Ba abin tinqaho da kafa hujja ne ga manufarsa ba. Domin kuwa tarihi ya tabbatar da cewa ba a tava nasara a kan Abubakar da Umar da Xalhatu da Zubairu da wasunsu da dama daga cikin Sahabbai ba. Duk maganar guda ce. Idan kuma ma dai har an tava nasara a kansu, tarihi bai faxa ba. Kamar yadda yake yiwuwa ya kasance an tava nasara a kan Alin, amma tarihi bai gano ba balle ya tsegunta wa duniya.

Muna da yaqinin cewa, waxancan Sahabbai ba su tava cin qasa a fagen fama ba. Don ko a yaqoqa biyu waxanda musulmi suka haxu da jarabawa a cikinsu, wato yaqin Uhudu da na Hunainu, ba a yi nasara a kan waxannan Sahabbai ba. Abin da littafan tarihin yaqe-yaqe suka ambata, shi ne Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma na tare da Annabi cirje, cirjiyar matashin zaki, har mazaje suka gama cin qasa su kan suna sama. Duk kuwa wanda ya ce an kayar da su a wannan rana, to, ya yi qarya. Amma Usmanu Raliyallahu Anhu ya bi sahun sauran waxanda Allah ya ce, ya gafarta masu don sun ja da baya.

Amma cewar da xan Shi’ar yayi Ali Raliyallahu Anhu bai tava bugun wani abu da takobinsa ba face ya gama da shi. Ba mu da masaniya akan ingancin wannan magana ko rashin ingancinta. Babu wata riwaya ingantatta a hannunmu da za mu iya rosa wannan da ita. Amma da za’a sami wani ya ce Khalidu ne da Zubairu da Bara’u xan Malik da Abu Dujanata da Abu Xalhata da makamantansu waxanda ba su tava bugun wani abu da takobinsu ba face sun gama da shi, ka ga an yi kunnen doki kenan. Musamman da yake kasancewar irin su Khalidu xin, da shi Bara’u mafi shahara da wannan irin jaruntaka kamar yadda masana tarihi za su iya faxa. Don kuwa har an riwaito cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Khalidu wani takobi ne daga cikin takubban Allah, wanda Allah ya zare a kan mushrikai.

Babu wanda zai ji wani qaiqayi ko ya yi wani kokwanto, idan aka ce, wanda Manzon Allah ya siffanta da kasancewa takobin Allah, ba ya saran abu face ya gama da shi. Aka kuma taras da cewa Khalidun nan ya kashe kafirai ba adadi a fagen fama. Kuma har ya koma ga Allah bai tava gudu daga wurin yaqi ba. Wannan magana ta fi qanshin gaskiya, da an jingina ta gare shi.

Xan Shi’ar kuma ya ce wai, da yawa Ali Raliyallahu Anhu ya yaye wasu baqqan ciki daga fuskar Manzon Allah. Sai mu ce, ko dai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke yaye baqqan ciki daga reshi, shi da sauran Sahabbai. Ai ko Abubakar da Umar Raliyallahu Anhuma ba wanda aka riwaito ya tava yaye wani baqin ciki daga fuskar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama su ma da ko Antaru ya san da su a fagen fama.

Amma ya tabbata a tarihi cewa, watarana Mushrikan Makka sun yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama qofar rago da nufin su kashe shi, sai Abubakar Raliyallahu Anhu ya daka masu tsawa yana cewa: Ya za ku kashe mutum don kawai ya ce: “Allah ne Ubangijina”? A sanadiyyar haka suka yi wa Abubakar duka matsananci. Amma ba a riwaito cewa Ali Raliyallahu Anhu ya bai wa Manzon Allah irin wannan kariya ba.

Shi kuwa kafa hujja da xan Shi’ar ya yi da kwanciyar da Ali Raliyallahu Anhu ya yi a kan shimfixar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a madadinsa, mun faxi cewa, Ali na da yaqinin ba abin da zai same shi. Don Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba shi tabbacin haka.


6.5.1 Ba Don Ali ne Kawai Aka ci Badar ba!

Xan Shi’ar ya ce: a wajen yaqin Badar, yaqi na farko a tarihin musulunci, wanda aka yi shi a farkon wata na goma sha takwas bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya isa Madina. A lokacin Ali Raliyallahu Anhu na xan shekaru ashirin da bakwai, ya kashe mutum talatin da shidda shi kaxai ransa. Adadin da ya fi rabin abin da aka kashe a wurin yaqin na kafirai. Yana kuma da hannu a cikin kashe sauran adadin.


Martani:

Ko shakka babu Ali ya yi bajinta a ranar Uhudu. Amma wannan magana ta xan Shi’a akwai qarin gishiri a cikinta. Kuma babu wani daga cikin malaman da ake iya dogara da riwayarsu wanda ya anbace shi. Jahillai ne kawai maqaryata suka kitsa ta.

Iyakar abin da masana suka ce shi ne, mutum goma sha xaya ne kawai aka tabbatar da Ali Raliyallahu Anhu ya kashe shi kaxai ransa, a wannan rana. Akwai kuma mutum shida da ake jin ba shi ne ya kashe su ba. Sannan akwai wasu mutane uku da ake da tabbacin Ali Raliyallahu Anhu yana da hannu a cikin kisansu su ma, a ranar. Wannan shi ne abin da malamai masu gaskiya irin Ibnu Hisham, da Musa xan Uqbata da Amawi suka ambata.

To, in ya yi wannan sai dole ne ya zamo halifan farko?


6.5.2 Kuma Wai a Hannunsa ne Aka ci Nasara a Uhudu

Xan Shi’ar ya ce: Gaba xayan mutane sun dare wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a ranar yaqin Uhudu in banda Ali. Sai fa wasu ‘yan tsiraru da suka dawo masa daga bisani, irinsu: Asimu xan Sabitu da Abu Dujanata da Sahalu xan Hunaifu. Sai kwana uku ne Usmanu xan Affana ya iso wurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Sai Annabin ya ce masa: Ai alqalami ya riga ya bushe. Kuma Malaiku sun cika da mamakim Ali a wannan rana. Ga ma abin da Jibrilu ke cewa a lokacin da yake komawa zuwa sama: “Lallai ba takobin qwarai bayan Dhul Fiqar (takobin Ali), Babu wani namiji kuma yau sai Ali”.

Xan Shi’ar ya ci gaba da cewa: Mafi yawan mushrikan da aka kashe a wannan yaqi, Ali Raliyallahu Anhu ne ya kashe su. Kuma nasarar da aka samu, a hannunsa ne aka same ta.

Kuma wai Qaisu xan Sa’ad ya ce: Na ji Aliyu Raliyallahu Anhu na cewa: An kai mani bugu sau goma sha shida a ranar yaqin Uhudu. Huxu daga cikinsu suka kai ni qasa. Sai wani mutum mai kyakkyawar fuska da kyakkyawar kama, ya zo mani da daddaxan qanshi, ya kama kafaxata ya tayar da ni. Sannan ya ce mani: Ka fuskance su, ka yaqe su a cikin xa’ar Allah da xa’ar Manzonsa, don suna cikin yarda da kai. Ali ya ce: Sai na zo na gaya wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, shi kuma ya ce mani: Ya kai Ali! Baka gane wannan mutum ba? Na ce masa: Eh, ban gane shi ba. Amma dai ya yi mani kama da Dihyatul Kalbiyyu. Daga nan sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Allah ya sanyaya zuciyarka ya kai Ali. Ai wannan mutum Jibrilu ne.


Martani:

Akwai qaryace-qaryace a cikin waxannan maganganu da dama, irin waxanda babu mai yarda da su sai wanda bai san tarihin musulunci ba. Na kuma yi mamakin irin yadda xan Shi’ar ke ratato tatsuniya kamar yana magana da wanda bai san abin da ya gudana a tarihin yaqe-yaqen musulunci ba.

Babbar illar qarya ta haxu da jahilci. Ai ba musulmin da bai san cewa ba wata nasara da musulmi suka yi a wannan yaqi ba. Gaskiya ne musulmi sun sami nasara a karon farin a ranar. Domin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci dakaru da su tsare mashigin dutsen da ake kira Jabalur Rumati, ya ce kuma kada wanda ya bar wurin ko da musulmi sun yi nasara ko an yi ta a kansu.

Samun nasarar musulmi a kan mushrikai ke da wuya, sai wasu daga cikin musulmi suka yi kururuwa: Ganima! Ganima!! Kwamandansu Abdullahi xan Jabir ya ce masu: Kada wanda ya kuskura ya tafi xibar ganima daga cikinku. Amma ina! Qaddara ta riga fata. Sai suka qi saurarensa. Gangarowarsu wurin ganimar ke da wuya sai mushrikai suka kewayo masu ta baya a qarqashin jagorancin Khalidu xan Walidu, kafin ya musulunta. Sai kuma suka ji kamar ana cewa: An kashe Muhammad! An kashe Muhammad!! Ashe Shexan ne ke wannan magana ba su sani ba. Nan take wuri ya ruxe.

Mutane ko suka ci tuwon kare, har ya kasance ba a bar kowa a tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba sai mutane goma sha biyu daga cikin Sahabbai, waxanda Abubakar da Umar na daga cikinsu.

Wannan rana ta kasance ranar jarabawa da fitina ga musulmi. Mushrikai suka kama hanyar komawa suna masu nasara a kan musulmi. Saboda daxi ya yi masu yawa ma sai da suka yi kamar su dawo su sake afka wa musulmi a cikin birnin Madina, amma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya sa musulmi suka hargage su.

Wani abin da kuma tarihi ya tabbatar shi ne: Aliyu da Abubakar da Umar Raliyallahu Anhum babu xaya daga cikinsu da ya kasance yana kariyar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a ranar. Gaba xayansu suna arangama ne da arna. Amma ba su gudu ba. Kuma a wannan yaqin an ji wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama rauni a goshinsa. Haka ma Sahabbai da dama. Amma lafiya lau Aliyu Raliyallahu Anhu ya fita.

Haka kuma cewar da xan Shi’ar ya yi wai Ali Raliyallahu Anhu ya ce: An kai mani bugu sau goma sha shidda a ranar yaqin Uhudu, huxu daga cikinsu har sun kai ni qasa.., ita ma qarya ce yake yi wa Ali Raliyallahu Anhu, domin babu wani littafi daga cikin sanannun littafai a wurin ma’abuta ilimi da ya kawo wannan magana, ballantana a samu isnadinta, ko a inganta ta. Abin da ya inganta a wannan yaqi ta wannan fuska shi ne, an yi wa Manzon Allah da wasu da yawa daga cikin Sahabbai rauni. Amma Ali ba wanda ya ce an yi masa ko qwalzane.

Ga abin da malam xan ishaka ke cewa: A lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya isa bakin sansanin sai Ali xan Abu xalib ya fito ya tare shi da gugar ruwa da ya xebo daga marmaro. Ya kawo ma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama don ya sha. Sai ya ji wani wari a cikinsu. A maimakon ya sha, sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya wanke jinin da ke fuskarsa da shi, ya kuma zuba saura a fuskarsa yana cewa: “Fushin Allah ya tsananta ga waxanda suka fitar da jini daga fuskar Manzonsu”.

Sai maganarsa ta cewa, wai, sayyidina Usman ya zo wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bayan kwana uku. Wannan ma qarya ce tuburan. Haka ma abin da ya hikaito Jibrilu na cewa, wai, a lokacin komawarsa zuwa sama bayan gama yaqin. Takobin ma da aka sani da sunan Dhul Fiqar ba na Ali ba ne. Takobin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne da aka ribata daga Abu Jahali ranar Badar.

Daga cikin abin da ke qara tabbatar da qaryar wannan magana har da cewa, Imamut Tirmidhi ya riwaito daga Ibnu Abbas cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ribaci takobinsa Dhul Fiqar a wurin yaqin Badar, kuma da shi ne ya yi mafarkin abin da zai faru a ranar yaqin Uhudu.

Ibnu Abbas ya ci gaba da cewa: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Na yi mafarkin wata gusxewa a bakin takobin nan nawa Dhul Fiqar, sai na fassara ta da wata gusxewa da za ta faru a cikinku. Na kuma gane ni a cikin mafarkin bisa wani rago, sai na fassara shi da runduna. Haka kuma na gane ni a cikin wata ganuwa, sai na fassara ta da birnin Madina. Na kuma ga ana yanke wata saniya. Na kuma san wallahi saniyar alheri ce.

Xan Abbas ya cika da cewa, duk abubuwan nan da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya faxa babu wanda bai faru ba.

Wannan magana ta takobi mai suna Dhul Fiqar, xaya ce daga cikin qaryace-qaryacen da wasu jahilai suka kitsa kamar cewar da suka yi Ali Raliyallahu Anhu ya mallaki wani takobi wanda idan ya kai baza da shi, takobin zai qara tsawo zira'i kaza da kaza, amma malamai na haqiqa sun daxe da sanin haka bata tava faruwa ba ga takobin Ali ko na waninsa. Da takobin Ali Raliyallahu Anhu na qara tsawo, da ko ya qara ranar yaqinsa da Mu'awiyah.


6.5.3 Ali a Yaqin Taron Dangi (Ahzab)

Xan Shi’ar ya ce: A ranar yaqin Ahzab, qare haqon kadarkon ke da wuya sai ga Quraishawa sun danno qarqashin jagorancin Abu Sufyana a cikin runduna ta mutum dubu goma, wadda ta haxa da qabilar Kinanata da mutanen Tihama. Sai kuma ga qabilar Gaxfanu da masu rufa mata baya daga cikin mutanen Najadu sun danno, suka yi sansani wa musulmi sama da qasa, kamar yadda Allah Ta’ala Ya ba mu labari: A lokacin da suka zo muku daga samanku da kuma qasa daga gare ku (33:10) sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita tare da musulmi dubu uku, suka saka kadarkon a gabansu, a waje xaya kuma Mushrikan can suka haxa kai da Yahudawa suka qara yawa. Hakan ta sa suka qara qwari, musamman ganin irin yadda Yahudawa suka dafa masu.

Daga nan Amru xan Abdu Wuddin da Ikrimatu xan Abu Jahali suka hau dawa kansu suka bi ta wata kafa a cikin kadarkon, suka tasar ma musulmi. Suka kuwa ce masu: Kule! Suna qalubalantar musulmi, ko akwai mai cewa Cas?

Nan take Ali Raliyallahu Anhu ya zabura wai, ya ce: An ce, cas! Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya hana shi. Ya ce masa: Ka fa san Amru ne. Sai da suka yi haka har sau uku. A na huxun sai Ali ya zabura ya yi cikinsa. Rashin arziqin Amru ya kai shi ga cewa: Kulenku! Wai sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa Ali Raliyallahu Anhu izinin tafiya ya fuskanci Amru a wannan karon. Shi kuma Amru da ya ga Ali Raliyallahu Anhu ya fito sai ya ce masa: Koma ya kai xan’uwana. Ba na son in kashe ka! Shi kuwa Ali Raliyallahu Anhu ya ce masa: Ka manta ka yi wa Allah alqawalin cewa babu lokacin da wani Baquraishe zai kira ka zuwa ga xayan biyu sai ka karva masa xaya?

Sai Ali ya kira shi zuwa musulunci. Amru ya karva masa da cewa: Ba ni da buqata ga wannan. Ali Raliyallahu Anhu ya ce: To, ina kiranka zuwa filin fama. Ga-ni-ga-ka. Amru ya ce: Uhum! Ali, ba na son in kashe ka fa. Shi kuwa Ali Raliyallahu Anhu ya karva masa da cewa: To, ni ina son in kashe ka.

Daga nan sai Amru ya sauka daga kan dokinsa, inji xan Shi’ar, suka yi karon battar karfe da Ali Raliyallahu Anhu. Nan take Ali Raliyallahu Anhu ya aika shi lahira. Sai kawai ka ga Ikrimatu ya juya, ya ranta cikin na kare. Sauran Mushrikai da Yahudawa duk suka ce qafa me na ci ban ba ki ba?

Wai kuma kan haka ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Abin da Ali ya yi wa Amru xan Abdu wuddin ya fi ibadar mutane da aljannu baki xaya.


Yüklə 2,75 Mb.

Dostları ilə paylaş:
1   ...   40   41   42   43   44   45   46   47   ...   51




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin