5.0 Zango Na Biyar
Hujjojin Shi’ah Daga Cikin Hadissai
5.1 Hadisin Liyafar Kiran Jama’a
Xan Shi’ar ya ce: mataki na uku ya qunshi dalilai daga cikin hadisai goma sha biyu, waxanda aka riwaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama:
Hadisi na farko shi ne, abin da gaba xayan mutane suka riwaito, inji shi, cewa, a lokacin da ayar da ke cewa:
ﭽ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﭼ الشعراء: ٢١٤
Kuma ka yi gargaxi ga danginka mafiya kusanci (26:214)
ta sauka, sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tara jimlar mutane arba’in na Bani Abdulmuxxalibi a gidan Abdulmuxxalibin, ya sa aka shirya masu abinci na mudun alkama xaya da qafar akuya, aka kuma tanadi sa’i xaya na madara.
Gaba xayan taron nan suka ci suka kuma sha, daga wannan qwaryaqwaryar liyafa suka yi hani’an ba tare da sun rage ta da komai ba. Hakan kuwa ya ba su mamaki matuqa, domin kuwa akwai da yawa daga cikinsu wanda ke iya zaunawa ya yi kalaci da tuttunar akuya ya taushe da wasakin ruwa ko yawansa na madara. Da haka sai jikinsu ya fara gaya masu cewa, lalle wataqila wannan alamar Annabcin Muhammadu ce. Qarewarsu ke da wuya sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Ya ku zuriyyar Abdulmuxxalibi! Ku sani lalle Allah ya aiko ni da saqon gaskiya zuwa ga halitta baki xaya. Ya kuma aiko ni zuwa gare ku musamman, don ya ce mani: Ka kuma yi gargaxi ga danginka mafiya kusanci (26:214). Saboda haka nake kiran ku zuwa ga waxansu kalmomi guda biyu, masu sauqin faxi ga harshe masu nauyi a kan sikeli, waxanda za ku iya mallakar Larabawa da Bobayi da su, sauran al’ummomi kuma su zama raqumi da akala a hannunku, ku kuma sami shiga Aljanna ku tsira daga wuta, duk a sanadinsu. Waxannan kalmomi su ne: Ku sheda babu wanda ya cancanci bauta sai Allah, kuma ni Manzon Allah ne. Wane ne daga cikinku zai karva wannan kira nawa a cikin wannan al’amari ya kuma taimake ni a kan tabbatar da shi, wanda zai zama xan’uwana, mataimakina kuma wanda zai gaji halifata bayan na wuce?. Duk suka yi tsit.
Sai Amirul Muminina (Ali Raliyallahu Anhu) ya ce: Ni, ya Manzon Allah! Zan taimake ka a kan wannan al’amari. Sai Manzon Allah ya ce masa: Zauna. Ya sake tambayar su, babu wanda ya ce masa uffan. Sai na sake tashi, inji Ali Raliyallahu Anhu na karva masa kamar yadda na karva da farko. Ya sake cewa in zauna. Ya kuma sake maimaita yekuwar can tasa, karo na uku, babu wanda ya ce masa qala daga cikinsu. Na sake tashi na karva masa cewa, Ni zan taimake ka ya Manzon Allah, a kan wannan al’amari. Sai ya ce mani: “Zauna. Kai ne xan’uwana, mataimakina kuma wanda zai gaji halifata bayan wucewata. Sai sauran mutanen suka tashi suna ce wa Abu Xalib: Ga irinta nan, gurinka ya cika, ka shiga addinin xan xan’uwanka, ga shi ya shugabantar da xanka a kanka.
Martani:
Za mu kore wannan hujja da dalilai guda takwas.
Dalili na farko:
Mene ne ingancin wannan labari?
Malaman da suka naqalci sirrin ilimin hadisi na sane da cewa, cewar da wannan marubuci ya yi gaba xayan mutane sun riwaito wannan hadisi qarya ce tsagwaronta.
Babu wani littafi daga cikin littafan malamai musulmi waxanda ake iya dogara da su a fagen ilimin riwaya, wanda ya zo da wannan Hadisi. Ina nufin gaba xayan Sihahu da Masanidu da Sunanu da Magazi da Tafsirai irin waxanda ake ambaton isnadi a cikinsu, waxanda kuma ake iya kafa hujja da su. A sane nake cewa, akwai wannan Hadisi a cikin wasu littafai na tafsiri, waxanda marubutansu ba su damu da ingancin hadisan da suke riwaitowa ba. A cikinsu akwai ingantattun hadisai da masu rauni, kamar tafsirin: Sa’alabi da Wahidi da Bagadadi, kai har ma da na Xabari da na Abu Hatim. Gaba xayan ma’abuta ilimi sun haxu a kan cewa kasancewar xaya daga cikin waxannan malamai ya riwaito hadisi, ba hujja ba ce a kan ingancinsa. To, tunda kuwa har ta tabbata cewa waxancan littafai akwai wake da shinkafa a cikinsu, to, dole ne a tabbatar mana da kasancewar wannan hadisi mai inganci ba mai rauni ba.
Dalili na Biyu:
Za mu iya karvar wannan qirarrar riwaya da xayan sharuxxa biyu; Ko dai marubucin ya kawo mana isnadin wannan hadisi, irin wanda masu ilimi ke kafa hujja da shi a lokacin da suke musayar ra’ayi, a cikin wata mas’ala ko da kuwa rava darni ce. Ko kuma ya kawo mana wani malamin hadisi xaya amintacce, irin wanda jama’ar musulmi ke dogara da maganarsa, wanda ya inganta wannan hadisi.
Na kawo waxannan sharuxxa ne, domin kuwa ga al’ada idan masana fiqihu guda biyu na musanyar ra’ayi a kan wata mas’ala ta furu’a, babu wanda zai tashi daga ra’ayinsa sai idan an kafa masa hujja da wani hadisi mai ingantaccen isnadi, irin wanda baya tunkuxuwa, ko wanda wani shahararre kuma amintaccen malamin hadisi ya inganta. Idan kuwa ba a samu xayan haka ba, sai dai a tashi kowa daga cikinsu yana a kan ra’ayinsa.
Wannan a cikin mas’aloli na hukunce-hukunce kenan. To ina ga sha’anin aqida wadda ita ce jigon addini? An wayi gari ana amfani da irin waxannan tatsuniyoyi ana sukar magabata da malaman wannan al’umma da manufar rosa shikashikan musulunci. Ba zai yiwu ba ko kaxan, a cikin irin wannan muhimmiyar matsala, mu karvi kowane hadisi wanda ba a san isnadinsa ba, kuma babu wani malami daga cikin jigajigan malaman riwaya da ya tabbatar da zamansa hadisi balle ingancinsa.
Dalili na uku:
Masana hadisi sun tabbatar da kasancewar wannan hadisi qiren qarya. Saboda haka ne ma, babu xaya daga cikinsu wanda ya riwaito shi a cikin littafansu waxanda ake kafa hujja da su. Kai ko wanda ke da qanqanuwar masaniya da ilimin hadisi, ya san wannan hadisi qarya ne.
Dalili na Huxu:
A lokacin da wannan aya ta sauka yawan maza a cikin zuri’ar Abdulmuxxalibi bai kai arba’in ba. Domin kuwa ayar ta sauka ne a garin Makkah, a farkon al’amari. Kuma har Manzon Allah ya bar duniya mazaje daga cikinsu ba su kai wannan adadi ba.
Dalili na Biyar:
Cewar da marubucin ya yi wai akwai da yawa daga cikin zuri’ar Abdulmuxxalibi wanda ke iya zaunawa shi kaxai ransa, ya yi kalaci da tuttunar akuya ya taushe da wasakin madara. Wannan magana qarya ce, don a tarihi ba a san banu Hashim da irin wannan mugun ci ba. Babu wanda aka ji labarin yana kalaci da tuttunar akuya ko ya shanye wasakin madara.
Dalili na Shida:
Cewar da marubucin ya yi wai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Wane ne daga cikinku zai karva wannan kira nawa a cikin wannan al’amari, ya kuma taimake ni a kan tabbatar da shi, wanda zai zama xan’uwana, mataimakina kuma wanda zai yi halifanci bayana”. Ko shakka babu wannan magana qarya ce suka yi wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama. Bai dace a jingina irin wannan magana gare shi ba. Dalili kuwa shi ne, imani da Allah da manzonsa tare da taimakon manzon a kan tabbatar da haka kawai, bai zama dalilin samun wancan matsayi.
Idan kuwa har tana zama dalilin hakan, ai gaba xayan muminai sun yarda da Allah da Manzonsa, sun kuma taimaki Manzon Allah a kan tabbatar da wannan aqida; sun sayar da rayuwarsu, sun saxaukar da dukiyarsu, sun bar garuruwansu, sun watsar da danginsu, sun yi haqurin xaixaicewa cikin garuruwansu bayan suna zaune wuri xaya. Sun yi haqurin walaqanci bayan a da su ne maxaukaka, sun yarda da talauci bayan a da suna cikin wadata, sun rayu cikin tsanani bayan a da suna cikin yalwa, ba don komai ba sai don yaxa addinin Allah da tabbatar da shi. Tarihin waxannan mazaje sannane ne a faxin duniya. Amma tattare da haka mafi yawa daga cikinsu ba su gaji halifar Manzon Allah bayan rasuwarsa ba.
To kuma idan har ta tabbata Manzon Allah ya faxi waccan magana a cikin mutum arba’in, to, ya ko kamata a ce gaba xaya ko mafi yawansu sun karva masa. To, idan xayan hakan ta faru, wane ne daga cikinsu zai gaje shi?
Dalili na Bakwai:
Wani abin da ke tabbatar da zaman wancan hadisi qarya, shi ne kasancewar ta tabbata cewa, Hamza da Ja’afaru da Ubaidatu xan Harisata duk sun karva wa Manzon Allah kamar yadda Ali ya karva masa a wancan lokaci.
Dalili na Takwas:
Abin da ya zo a cikin ingantattun littafan hadisi dangane da saukar waccan aya, ya sha bamban da abin da wannan marubuci ya kawo. Abin da ya zo a cikin Buhari da Muslimu shi ne: An samo daga Ibnu umar da Abu Hurairata daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama: A lokacin da ayar da ke cewa: Kuma ka yi gargaxi ga danginka mafiya kusancin (26:214) ta sauka, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kira Quraishawa suka taru, ya fara da su kafin sauran mutane, inda ya ce: Ya ku banu Ka’abu xan Lu’ayyu! Ku ceci kanku daga wuta, ya ku banu Murrata xan Ka’abu! Ku ceci kanku daga wuta, ya ku banu Hashimu! Ku ceci kanku daga wuta, ya ku banu Abdulmuxxalibi! Ku ceci kanku daga wuta. Ya ke Fatima ‘yar Muhammadu! Ki ceci kanki daga wuta. Ku sani ba ni iya shiga tsakaninku da Allah. Iya abin da nake iya yi maku na haqqin dangantaka da zumunta zan yi”.
5.2 Hadisin Ghadir ba Hujja ne ba
Hadisi na biyu a cewar sa, shi ne: Ingantaccen hadisi xan asuli, wanda aka samo daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama cewa a lokacin da faxar Allah Subhanahu WaTa’ala ta sauka:
ﭽ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﭼ المائدة: ٦٧
Ya kai Manzo! Ka iyar da abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka (5:67).
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi magana da mutane a cikin huxuba, a wani wuri da ake kira Ghadir Khum, ya ce masu: “Ya ku jama’a! Ashe ba ni da iko da ku fiye da yadda kuke da iko da kanku?” Suka ce, tabbas kana da shi ya Manzon Allah. Sai wai ya ce: “To, duk wanda nake da iko da shi Aliyu na da iko da shi”. “Ya Ubangiji ka jivinci al’amarin wanda ya jivinci Ali, ka juya baya ga duk wanda ya juya masa baya, ka taimaki duk wanda ya taimake shi, ka kuma tozarta duk wanda ya tozarta shi”. Wai kuma daga nan sai Umar ya ce: “Ai daxa ta qare. Daga yau kai ne ubangidana kuma ubangidan gaba xayan Musulmi da muminai maza da mata”.
Mun riga mun ba marubucin amsa a kan wannan aya da wannan hadisi, tare da tabbatar masa da kasancewar yadda ya karkata akalar ayar, qarya. Don ayar ta sauka ne kafin hajjin bankwana da lokaci mai tsawo. Ita kuwa maganar da ya yi a Ghadir Khum ta kasance ne a ranar sha takwas ga watan Zul-hajji bayan ya kammala hajjinsa ya kama hanya zuwa gida. Watanni biyu bayan haka da wasu ‘yan kwanaki sai Allah ya karvi ransa. Kuma tarihi ya tabbatar da cewa babu wani abu na shari’a da ya sauka ga Manzon Allah zuwa ga mutane, a ranar da ya sauka a Ghadir Khum, daxa ko, abin ya shafi Ali Raliyallahu Anhu ne ko waninsa, a kan sha’anin shugabanci ko wani abu wanda ba shi ba. Babu ko xaya.
A sane muke cewa, Tirmizi ya riwaito wannan labari da kuma Ahmad a cikin Musnad nasa. Amma iyakar abin da Annabi ya ce shi ne: “Duk wanda nake abin jivintar sa, to Ali ma majivincinsa ne”. Amma abin da xan Shi’ar ya zo da shi na cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ci gaba da cewa: “Ya Ubangiji ka jivinci al’amarin wanda ya jivinci Ali, ka kuma bayar da baya ga duk wanda ya ba shi baya...” Ko shakka babu wannan qari ne kuma qiren qarya; Manzon Allah bai ce haka ba. Haka nan kuma cewar da ya yi wai Umar ya ce: “Daga yau kai ne ubangidan gaba xayan muminai maza da mata”. Shi ma wannan qarya ce tabbas.
To, fita batun ma wannan baki xaya. Ita kanta waccan magana da ya ce Annabi ya ce: “Duk wanda nake abin jivintar sa, to Ali ma majivincinsa ne” Babu ta a cikin Sihahu, illa dai wasu malamai kawai suka riwaito ta. Wasu malaman kuma kamar su Buhari da Ibrahimul-Harbi da wasu da dama da cikin masana ilimin hadisi, suka tsaya cik a kan wannan sha’ani. A qarshe dai duk sun yi suka a cikin hadisin tare da raunana shi. Imamu Ahmad ne kawai aka samu ya inganta hadisin kamar yadda Tirmizi ya yi. Malam Abul-Abbas xan Uqdata ma har littafi ya wallafa inda ya tattara hanyoyin da aka samo hadisin ta su.
Ka ga tun daga nan mu Allah Ya hutar da mu, amsarmu ta samu qarin qarfi. Wato idan har ta tabbata Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama bai faxi wannan magana ba, to batu ya qare; Ummu ta gaida Aisha. Idan kuwa har ya faxe ta, to, lalle ba yana nufin Ali Raliyallahu Anhu zai gaji matsayinsa ne bayan ya wuce ba, don babu wani harafi a cikin maganar da ke nuna haka. Al’amari ko mai girma irin wannan lalle ne idan za a yi magana a kansa a yi ta dalla-dalla.
Ko shakka babu wannan hadisi baya nufin tabbatar da halifanci ga Ali Raliyallahu Anhu. idan kuwa don taqamar kalmar “Maula” ce, wadda Annabi ya yi amfani da ita a cikin hadisin, to, ta yi gabas ne shi kuwa xan Shi’ar ya yi yamma. Wannan kalma ta “Maula” da kalmar “Waliyi” xan Juma ne da xan Jumai; rawa xaya suke takawa. Don ka ga ai Allah Subhanahu WaTa’ala cewa Ya yi: Abin sani kawai majivincinku Allah ne da Manzonsa, da waxanda suka yi imani (5:55). A wata ayar kuma ya ce: Kuma idan kun taimaki juna a kansa, to, lalle ne Allah shi ne mataimakinsa, da Jibrilu da salihan Muminai. Kuma mala’iku a bayan wannan mataimaka ne (66:4). A cikin waxannan ayoyi guda biyu, Allah Subhanahu WaTa’ala ya bayyana cewa, akwai alaqa tsakanin shi da Manzonsa a gefe xaya, da salihan muminai a gefa xaya ta hanyar jivintar al’amari da taimakekeniya, gwargwadon iko da matsayin kowane vangare.
Wato jivintar al’amari da taimakekeniya a wannan tsakani, na nufin rahama da jinqai na ganin dama daga wurin Allah da Manzonsa zuwa ga muminai, da xa’a da bauta na yarda da amincewa daga wurin muminai zuwa ga Allah Subhanahu WaTa’ala. kamar dai yadda ta tabbata cewa tsakanin Allah Subhanahu WaTa’ala da muminai akwai son juna.
Kenan Allah shi ne majivincin al’amarin muminai kuma mataimakinsu. Don haka ne ma ya fitar da su daga cikin duhun kafirci zuwa ga hasken imani. To, tunda kuwa har haka ne, jivintar al’amari da taimakon Allah da na Manzonsa zuwa ga muminai, da kasancewar Ali Raliyallahu Anhu majivincin muminai na nufin so ne da qauna, savanin qiyayya da gaba. Irin wannan so da qauna ne kuwa, muminai ke yi wa Allah da Manzonsa gwargwadon matsayinsu. Babu kuwa wani mumini da ya fi wani a wannan matsayi. Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu kuwa na xaya daga cikin wanda ke so da qaunar muminai kamar yadda su ma suke so da qaunarsa.
A taqaice dai akwai banbanci matuqa tsakanin kalmomin Waliyyu da Maula waxanda muka qare sharhi a kansu, da kuma kalmar Wali. Kalmomi guda biyu na farko, kamar yadda bayani ya gabata, na nufin so da qauna, jinqai da taimako. Ita kuwa kalma ta biyu na nufin shugabanci. Kuma asalin waxannan kalmomi a tafsirin Larabci ba xaya ba ne.
Shi wannan hadisi da muke taqaddama a kansa ya zo ne da xayan waxannan kalmomi na farko, wato Al-Maula da Al-Waliyyu. A Hausance abin da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce shi ne: “Duk wanda yake akwai so da jinqai tsakanina da shi, to, a samu hakan a tsakaninsa da Ali”. Ba cewa ya yi: Duk wanda nake shugaba a gare shi, to Ali ya zama shugabansa ba.
Duk wanda ya fassara wannan hadisi da cewa, Manzon Allah na nufin ya zavi Ali Raliyallahu Anhu a matsayin halifansa, ya yi kuskure ba xan qarami ba. Wilayar da Annabi ke nufi irin ta so da qauna, na tabbata ne a matakin musaya tsakanin vangarora biyu: Wato soyayya da qawanceceniya. Kamar yadda muminai ke son Allah, shi kuma yana son su.
Kuma kasancewar Manzon Allah na da iko da muminai fiye da yadda suke da shi da kansu, daraja ce wadda shi kaxai ya kevanta da ita a duniya a matsayinsa na Annabi.
5.3 Hadisin Matsayin Ali
Hadisi na uku a cewarsa, shi ne faxar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da yake ce ma Ali: “Matsayinka a wurina kamar matsayin Haruna ne a wurin Annabi Musa. Sai dai ka sani babu wani Annabi a bayana”. Wai da wannan zance ne Manzon Allah ya tabbatar wa Ali Raliyallahu Anhu da irin gaba xayan martabobin da Haruna ke da su, a wurin Annabi Musa ba tare da rage komai ba. Daga cikin martabobin na Haruna kuwa akwai kasancewarsa halifan Annabi Musa, a lokacin da yake raye. To, da kuwa ya rayu bayan rasuwar Annabi Musa, da lalle ne zai gaji halifarsa, wanda savanin haka kuwa, zai tabbatar da wata kasawa a cikin zatinsa. Tunda kuwa har Haruna ya waqilci Annabi Musa a matsayin shugaban bani Isra’ila, a sakamakon ‘yar tafiyar da ya yi don ganawa da Allah, to, babu wanda ya cancanci zama halifan Annabi Musa bayan rayuwarsa kamar shi Harunan.
Martani:
Amsarmu a kan wannan magana ita ce: Tabbas wannan hadisi gaskiya ne. Don Buhari da Muslimu da wasunsu, sun riwaito shi. Kuma Manzon Allah ya faxi wannan magana ne a lokacin da zai tafi yaqin Tabuka. Amma wannan ba abin tinqaho ba ne, don ba a kan sa aka fara ba. A duk lokacin da aikin Umara ko Hajji ya zo, ya kan waqilta wani daga cikin Sahabbai ya tsare birnin Madina. Kamar yadda ya waqilta Sayyidina Umar a lokacin da zai je yaqin da aka sani da suna Gazwatu Dhi Amrin. Ya kuma waqiltar da Bashiru xan Abdulmundhir a lokacin da zai je yaqin banu Qainuqa’a. Ya waqilta Abdullahi xan Ummu Maktumi a lokacin da ya je Fur’u don yaqar Quraishawa. Malam Muhammadu xan Sa’ad da waninsa duk sun ambaci wannan.
A taqaice dai, sanannen abu ne a tarihin musulunci cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai tava fita ya bar birnin Madina haka nan sake ba. Lalle ne ya waqilta wani ya tsare ta. Kuma littafan tarihi cike suke da jerin sunayen Sahabban da ya kan waqilta lokaci-lokaci don wannan aiki. Sau biyu Manzon Allah na tafiya aikin Umara daga Madina; Umarar “Hudaibiyya” da ta rankonta, don da ya je a karon farko bai samu yinta ba, ya dawo bisa ga yarjejeniyar da aka sani da suna Sulhin Hudaibiyyah. Ya kuma tafi hajjin bankwana. Su kuwa yaqoqa ya yi fiye da ashirin. A duk waxannan tafiye-tafiye Manzon Allah yakan naxa wani Sahabi ne ya tsare gari kafin ya dawo.
Wannan waqilci da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya naxa Ali Raliyallahu Anhu a wannan lokaci, shi ne mafi rauni da qarancin daraja bisa ga waxanda suka gabace shi. Dalili kuwa shi ne, a duk waxancan lokutan a kan taras cewa a cikin birnin na Madina akwai mazaje da dama, da shi wannan waqili zai shugabanta. Amma a wannan karo saboda girman Tabuka, Manzon Allah bai xauke wa kowa nauyin halartar yaqin ba, sai fa mata da qananan yara da tsofaffi. Sai ko marasa lafiya in akwai. Sannan an bar munafukai da wasu mutane guda uku da suka yi gangancin rashin fita, kuma daga bisani Allah ya yi masu afuwa.
Wannan dalili ne ya sa Sayyidina Ali Raliyallahu Anhu ya fito yana kuka. Ya tunkari Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Ya Manzon Allah! Za ka bar ni a gari ba kowa ciki sai mata da qananan yara?
Ka ga tun a nan taba ta banbanta da garin gero. Don shi Haruna rundunar bani Isra’ila ce gaba xayanta Annabi Musa ya bar masa kulawa da ita, shi kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai bar komai ba a gida sai tattaka da baragurbi, in ka xebe shi sayyidina Alin xin Raliyallahu Anhu.
Kai aje ma duk wannan, idan muka dawo ga tsurar ruwan zatin harshe, za mu ga cewa, a duk lokacin da wani ya ce: matsayin wannan abu kamar ya ce ne: Abu kaza ya yi kama da abu kaza. Shi kuwa irin wannan, kamantawa ne kawai. Hakan ba ta nufin abubuwan guda biyu sun yi kunnen doki a cikin komai. A’a, yanayin zatin zancen ne alqali.
Dubi abin da Buhari da Muslimu suka riwaito, a lokacin da Manzon Allah ya shawarci Sayyidina Abubakar da Sayyidi Umar Raliyallahu Anhuma a kan makomar fursunonin yaqin cin garin Makkah, Abubakar ya ce, su fanshi kansu. Umar kuma ya ce, a aika su lahira. Sai Manzon Allah ya ce: Ku bari in yi maku fashin baqin matsayin waxannan mazaje biyu: Kai Abubakar ka yi kama da Annabi Ibrahim a cikin wannan shawara taka. Don cewa ya yi: Sa’annan wanda ya bi ni, to, lalle shi, yana daga gare ni, kuma wanda ya sava mini, to lalle ne kai mai gafara ne, mai jinqai (14:56). Ka kuma yi kama da Annabi Isa, a inda ya ce: Idan ka azabtar da su, to lalle ne su bayinka ne, kuma idan ka gafarta masu, to, lalle kai ne Mabuwayi Mai hikima (5:118). Kai kuwa Umar ka yi kama da Annabi Nuhu a cikin shawararka, inda ya ce: Ya Ubangiji! Kada ka bari a kan qasa, daga cikin kafirai, ko wanda ke zama a cikin gida (71:26). Ka kuma yi kama da Annabi Musa inda ya ce: Ya Ubangiji ka shafe a kan dukiyoyinsu kuma ka yi xauriya a kan zukatansu ta yadda ba za su yi imani ba har sai sun ga azaba mai raxaxi (10:88).
Kwatantawar da Manzon Allah ya yi wa waxannan Sahabbai da waxannan Annabawa ta fi wadda ya yi wa Ali da Haruna. Don darajar Haruna ba ta kai ga ta Nuhu da Ibrahimu da Musa da Isah ba. Don waxannan su ne Ulul Azmi, mafi daraja daga duk manzanni. Amma ba a tava jin wani ya ce darajar Sahabban daidai take da ta Annabawan ba. Iyakar abin da kwatancen ke nufi shi ne, Sahabban sun yi kama da Annabawan a cikin tsanantawa ko sauqaqawa a cikin al’amarin Allah.
Zahiri da baxinin wannan hadisi na nuna cewa, Manzon Allah na nufin matsayin Ali Raliyallahu Anhu a wurinsa, a daidai wannan lokaci, kamar matsayin Haruna ne a wurin Annabi Musa, a lokacin da ya waqilce shi bayan da ya tafi ganawa da Maxaukakin Sarki. Haka kuma wannan waqilci ba wata martaba ce da Ali Raliyallahu Anhu ya kevanta da ita ba. Don ya yi waxansu waqilce-waqilcen waxanda suka fi wannan xaukaka. Ka ga zancen a xauki wannan waqilci wasu kayan gabas bai taso ba.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai kevance Ali Raliyallahu Anhu da wannan matsayi ba. Ya dai gaya masa wannan magana don sanyaya ransa, ganin irin yadda ya fito yana kuka a kan barin sa tsaron mata da qananan yara. Kuma shi ya sa bai yi irin wannan magana ga sauran waxanda ya waqiltar kafin Ali ba. Don su ba su fahimci cewa akwai wata naqasa cikin shugabanci da waqilcin da aka sa su ba. Don haka, hadisin bai nuna cewa, ba mai irin wannan matsayi na Haruna a wurin Musa sai Ali.
Wasu kuma daga cikin ‘yan Shi’ah cewa suke yi, wai Manzon Allah ya tabbatar wa Ali da dukan matsayin da Haruna ke da shi, ban da na Annabta. Wannan magana ba gaskiya ba ce. Ce wa Ali da Manzon Allah ya yi: “Ba ka son ka zama a wurina kamar yadda Haruna yake a wurin Musa?” Na nuni kai tsaye a kan cewa ya faxi wannan magana ne kawai don ya rarrashi Ali, ya kuma nuna masa fahimtar da ya yi wa al’amarin ba haka take ba. Haka kuma akwai qarfafa guiwa da washe tunani zuwa ga Ali, don Manzon Allah ba ya da niyyar cire shi daga waqilcin.
Kuma ba ka ganin cewa Manzon Allah ya yi: “Kamar yadda Haruna yake a wurin Musa”? Yana nufin kama ne kawai. Don haqiqanin matsayin Haruna a wurin Musa ba ya samuwa ga wani. Kamar dai yadda ya kamanta Sahabban can biyu da Annabawan can huxu a hadisin Buhari da Muslimu.
Wani abin da ke qara tabbatar da haka, shi ne tura Ali Raliyallahu Anhu da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi don ya bi Sayyidina Abubakar wurin aikin hajji inda yake waqiltar Manzon Allah, bayan dawowarsu daga yaqin Tabuka. Da ya riski Abubakar a hanya, ya sanar da shi saqon da yake tafe da shi, sai Abubakar xin ya tambayi Ali Raliyallahu Anhu cewa: To, a matsayin shugaba ka zo, ko mabiyi? Ali ya karva masa da cewa, A’a, ni mabiyi ne. Haka kuwa aka yi. Ali ya ci gaba da zama qarqashin shugabancin Abubakar, yana bin sa sallah, yana kuma biyar umurninsa, har ma Abubakar xin ya sa shi maimata wa mutane abin da yake faxa: “Ku saurara ya jama’a! Daga bana sai bana. Kada mushriki ya sake zuwa hajji. Kada kuma wanda ya sake yin xawafi tsirara”.
Kuma xan Shi’ar ya ce wai, waqiltar da Ali Raliyallahu Anhu ya yi wa Manzon Allah yana raye saboda tafiyar da ya yi wurin yaqi ta ‘yan kwanuka na tabbatar da kasancewar sa mafi cancanta da gadon halifanci bayan rasuwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Amsa a nan ita ce, ai kafin waqiltar da Ali Raliyallahu Anhu a wannan lokaci, an waqiltar da wasu Sahabbai, waqilci irin wanda kuma ya fi wanda Ali ya yi martaba, don jama’ar da suka kula da su ta fi wadda Ali ya kula da ita qima. Kuma bayan an dawo daga yaqin Tabuka ai wani Manzon Allah ya waqilta kafin ya je hajjin bankwana ba Ali ba, don ya tsare garin Madina. Waqilcin kuwa da aka sa Ali ya yi na tsare garin Madina bai fi wanda sauran Sahabbai suka yi kafinsa da bayansa ba, balle hakan ta zama dalilin zamansa halifa bayan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama.
Idan kuwa ci gaba da waqilci har lokacin da Manzon Allah ya canza mutum ne sharaxi, to, xorewar shugabancin wanda aka shugabantar qarshe ya fi cancanta. Wato wanda ya waqilci Manzon Allah a hajjin bankwana, ba wanda ya waqilce shi kafin sa ba.
A taqaice dai, kamar yadda muka faxa ba Ali Raliyallahu Anhu ne kawai Manzon Allah ya waqilta wa riqon garin Madina ba, kuma hakan ba ta nuna Ali ya fi sauran waxanda aka waqiltar xin, ko kuma hakan ta zama hujja a kan shugabancinsa bayan wucewar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Wannan xaukaka ta waqiltar Manzon Allah ta shafi duk gaba xayan waxanda suka tava yin ta. Amma saboda jahilcin ‘yan Shi’ah sai su yi hankaka; su taqaita darajojin a kan Ali Raliyallahu Anhu shi kaxai. Tattare da cewa akwai da yawa daga cikin Sahabbai waxanda suka fi shi kamala. Haka dai dama suka saba; karkata akalar nassosa da tabbatattun abubuwa na tarihi.
Dostları ilə paylaş: |