8.0 Zango Na Takwas: Ayubban Sauran Halifofi, InJi Shi: ............................ 500
8.1 Wai Abubakar Ba Shi Da Lafiya: ............................................................... 501
8.2 Wai Mubaya’ar Abubakar Ba Ta Yi Ba: .................................................... 504
8.3 Wai Halifofi Uku Jahilai Ne!: ..................................................................... 505
8.4 Kuma Wai Halifofi Sun Yi Abin Kunya!: ................................................... 505
8.5 Wai Halifofi Uku Sun Bauta Ma Gumaka: .................................................. 506
8.6 Wai Abubakar Ya Nemi Yin Murabus: ........................................................ 507
8.7 Kuma Wai Abubakar Ya Yi Nadama!: ......................................................... 507
8.8 Wai Abubakar Ya Faxa Gidan Fatima Ba Sallama!: ..................................... 508
8.9 Wai Halifofi Sun Fice Daga Rundunar Usamatu!: ........................................ 509
8.10 Wai Abubakar Bai Tava Jagoranci A Zamanin Manzon Allah Ba!: ........... 510
8.11 Wai Manzon Allah Ya Tuve Abubakar Daga Amirul Hajji!: ...................... 510
8.12 Kuma Wai Umar Bai Iya Hukunci Ba!: ....................................................... 512
8.13 Wai Umar Ya Qago Sallar Asham: .............................................................. 513
8.14 Wai Musulmi Sun Haxu A Kan Kashe Halifa Usman!: ............................... 514
9.0 Zango Na Tara: Rashin Cancantar Abubakar Ga Halifanci A Wurinsu:......... 516
9.1 Rashin Samun Ijma’i A Kansa: ....................................................................... 516
9.2 ‘Yan Shi’ah Ba Su Yarda Da Ijma’i Ba :.......................................................... 519
9.3 Wai Kuma Al’umma Ba Ta Haxu Kan Abubakar Ba!: ................................... 520
9.4 Wata Suka Ga Ijma’i: ....................................................................................... 521
9.5 Kuma Wai Zaven Abubakar Ya Sava Ma Nassi: ............................................. 522
9.6 Suka Ga Hadisin Koyi Da Abubakar Da Umar: ......................................... 522
9.7 Wai Hijirarsa Tare Da Annabi Ba Daraja Ba Ce! : ..................................... 524
9.8 Gaba Ta Koma Baya: .................................................................................. 531
9.9 Babu Shakka Abubakar Ya Damu: ............................................................. 534
9.10 Abubakar Ne Dai Ayar Ke Nufi: .............................................................. 537
9.11 Shi Wannan Ayar Ke Nufi: ....................................................................... 538
9.12 Abubakar Da Manzon Allah A Ranar Badar: ............................................ 542
9.13 Abubakar Ya Yi Hidimar Manzo Da Dukiyarsa: ....................................... 544
9.14 Abubakar Xin Ne Dai Liman: ..................................................................... 547
9.15 Darajojin Abubakar A Cikin Hadissai: ....................................................... 549
GABATARWAR CIBIYAR AHLUL-BAITI DA SAHABBAI
Godiya ta tabbata ga Allah wanda aikin alheri ba ya kammala sai da taimakonsa. Muna godiya a gare shi bisa taimakon da ya yi mana na kammala wannan aiki mai tarin albarka.
Babbar manufar da aka kafa wannan cibiya a kanta ita ce, bayyana gaskiyar Allah game da kyakkyawar dangantakar da ta wanzu a tsakanin Ahlul-Baiti, iyalan gidan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da kuma Sahabbai, wato almajiransa. Babu shakka sanin wannan kyakkyawar dangantaka na qara mana sanin qoqarin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wajen shiryar da al’ummarsa, da nasarorin da ya samu a cikin aikin da Allah ya xora ma sa na yin tarbiyyar jama’arsa. Kamar yadda Allah ya ce:
ﭽ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲ ﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﯸ ﯹ ﯺ ﯻ ﯼ ﭼ آل عمران: ١٦٤
Haqiqa Allah ya yi baiwa a kan muminai a lokacin da ya tayar da manzo a cikinsu, daga kawunansu, yana karanta ma su ayoyin Allah, yana tsarkake su, yana ilmantar da su littafin (Alqur’ani) da Hikima (Sunnah), kodayake sun kasance a cikin bayyanannen vata gabanin haka. Ali Imran: 164.
Tsarkake su da Allah ya xora wa Manzo yi, shi ne tarbiyyarsu. Don haka duk wata suka ga tarbiyyar tasu to, suka ce ga Manzon Allah xin kansa. Kuma ma dai Alqur’ani ya ba mu tabbacin wanzuwar so da qauna da rahama a tsakaninsu. Kamar in da Allah yake cewa:
ﭽ ﭑ ﭒ ﭓﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭼ الفتح: ٢٩
Muhammadu Manzon Allah ne. Kuma waxanda ke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai, masu jinqayi a tsakanin junansu. Al-Fathi: 29
Da kuma in da yake cewa:
ﭽ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭼ الأنفال: ٦٢ – ٦٣
(Allah) shi ne wanda ya qarfafe ka da taimakonsa da kuma muminai. Kuma ya haxa zukatansu. Al-Anfal: 62-63.
Wannan cibiya ta samu littafin nan na Shehun musulunci Ibnu Taimiyyah daidai da wannan manufa, domin ya bayyana gaskiyar wannan al’amari ta hanyar hujjoji bayyanannu masu qwari.
Wannan Littafi
Babu shakka Ibnu Taimiyyah ya yi bajimin qoqari a cikin wannan littafi, kamar yadda ya saba yi a sauran littafansa waxanda suke matsayin taurari a samaniyar ilimin addini. Muna kyautata zaton cewa, babu mai hankali da basira da zai karanta wannan littafi face ya amfana da shi ta fuskar gano bakin zaren duk abubuwan da ake taqaddama a kansu kan matsayin Sunnah da Shi’ah a addini. Malamin ya sanya haquri da juriya kamar yadda ya sa ilimi da basira a cikin mayar da martanin abubuwan da ‘yan Shi’ah suke faxa a kan Sahabbai. Ya yi shi ta hanyar tattaunawa yana mai mayar da martani a tsanake kan littafin da jagoran ‘yan Shi’ar zamaninsa Ibnul Muxahhir ya wallafa mai suna Minhajul Karamati Fi Isbatil Imamati. Malamin ya bi littafin daki-daki yana tattaunawa a kan dalilan da aka kawo.
Da yawan mutane sukan yi zaton cewa, ‘yan Shi’ah na riqe da hujjoji ko aqalla shubhohi masu qarfi, waxanda ke da wahalar tunkuxewa in ba ga malamai ba. Amma wanda ya karanta wannan littafi take zai gano lamarin ba haka yake ba. Domin kuwa mawallafin ya tabbatar a aikace cewa, ba su da wata hujja ko guda qwaqqwara. Bil hasili ma, duk a cikin qungiyoyin da ke jingina kansu ga musulunci babu marasa hujja irinsu. Domin su ne waxanda duk hujjar da suka kafa, da an dube ta da kyau ana iya amfani da ita wajen hujjace su. Ya kuma ba da haske game da dabarun da suka cancanta mai tattaunawa da su ya bi don lurar da su gaskiya. Kamar in da ya ke cewa:
To, a wajen jayayya, idan musulmi ya tattauna da Kirista ba zai iya faxin wani abu game da Isa Alaihis Salamu ba face gaskiya. Amma in kana son ka fito da jahilcin Kirista da rashin hujjarsa, to, sai ka qaddara jayayyar a tsakanin sa da Bayahude, ka koma gefe ka saurare shi. Idan har Kirista ba zai iya kare Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba, to, duk zargin da ya yi masa zai tarar Bayahude yana yi wa Annabi Isah Alaihis Salamu irinsa. Kuma duk hujjar da zai kawo don ya kare Annabi Isah Alaihis Salamu wannan hujjar ta fi kare Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama daga shi nasa zargin. Saboda haka, in zargin da Bayahude yake yi wa Annabi Isah Alaihis Salamu qarya ne, to, zargin Kirista ga Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama ya fi zama qarya.
To, wannan shi ne abin da ke tsakanin Ahlus-Sunnah da ‘yan-sha-biyu ga lamarin Abubakar da Ali. Xan Shi’ar ba zai iya tabbatar da imanin Ali ba, da cewa shi xan aljanna ne, ballantana ya tabbatar da shugabancinsa sai fa in ya tabbatar da haka ga Abubakar da Umaru da Usmanu.
Don in ba haka ba duk lokacin da ya so ya tabbatar da wata daraja ga Ali, to, dalilai ba sa taimaka masa, kamar yadda in Kirista ya so ya tabbatar da annabcin Isa Alaihis Salamu ba zai iya ba sai in ya yarda da annabcin Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama, domin dalilai ba za su taimake shi ba.
Bisa ga haka, idan ka tattauna da wani daga cikin ‘yan-sha-biyu, to, qaddara masa tattaunawar tsakanin sa da Harijawa masu kafirta Ali da Nasibawa masu fasiqantar da shi. Harijawa sun tafi a kan cewa, Ali azzalumi ne, mai neman duniya, wanda ya nemi halifanci da qarfi, ya yaqi mutane a kansa. A garin haka kuwa ya kashe dubun dubatar musulmi, abin da ya hana cin nasarar mulkinsa. Ya kuma kasa samun abin da yake so na kevanta da mulki, sai magoya bayansa suka dare masa, suka yaqe shi har daga qarshe suka kashe shi.
To, ka ga wannan magana in qarya ce, to, ba shakka maganar xan Shi’ar a game da Abubakar da Umar ta fi ta zama qarya. In kuma har maganar xan Shi’ar a game da Abubakar da Umar daidai ne, kuma magana ce ta gaskiya, to, lalle ko maganar Harijawa a kan Ali ta fi cancantar zama gaskiya.1
Wannan littafi ya karva sunansa bisa gaskiya, domin mawallafin ya shimfixa qa’idodi masu tarin yawa a cikinsa, masu kuma amfani, waxanda ke bayyana tafarkin Ahlus-Sunnah a cikin sha’anin ilimi da aqida. Dubi waxannan haskakan maganganu nasa a matsayin misalai:
Ita dai magana duk wanda zai yi ta, wajibi ne ya yi ta akan ilimi da adalci, musamman in ta shafi mutuncin wani mutum musulmi kowane iri ne. Ba daidai ba ne a yi ta a kan jahilci da zalunci, kamar yadda ‘yan bidi’a ke yi a ko’ina. Dubi yadda ‘yan-sha-biyu ke bijirowa da mutane masu kusanci da juna ta fuskar girma da xaukaka, da zamansu waliyyan Allah, amma sai su raba su; wasu su ce ma’asumai ne da ko rafkanwa xayansu ba ya yi. Sauran kuma su ce masu fajirai ne ko fasiqai ko kafirai. Kai tsaye kana iya gane jahilcinsu da taqin saqar maganarsu. Kamar Bayahude ne ko Kirista, duk sadda xayansu ya buqaci tabbatar da annabcin Musa ko Isah Alahimas Salam, tare da yin suka ga annabcin Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama, ba zai iya ba, don nan take jahilcinsa da taqin saqar maganarsa zasu fito fili.
Da yawa cikin mabiyan Ali da na Usman na da ra’ayin cewa, Ali na da hannu cikin wannan juyin mulki da ya kai ga kashe Usman. Waxannan sun ce Ali na da hannu don ba su son Usman. Suna son su ce ko Ali ma ba ya sonsa. Waxancan su kuma sun ce Ali na da hannu don ba su son Alin. Suna son su shafa masa kashin kaji. Amma mafi yawan musulmi sun san qarya vangaroran biyu ke yi.2
Kasancewar Malam Sa’alabi na cikin malaman da ke amsa sunan Sunnah kawai bai isa hujja akan karva duk maganarsa ko da kuwa tana zancen darajar halifa Abubakar ne, sai fa in an tabbatar da ingancinta. Kamar dai xan Shi’ar yana son ne ya ce, ga wani malami nan daga cikinku na kafa muku hujja da shi, don ya faxi abin da ya zo daidai da ra’ayina. To, ai Ahlus-Sunnah gaskiya suke bi ba malamai ba. To, ta ya ya ruwayar fataken dare, mai maqoshin kolo a ruwaya, wanda ke yaki-halas yaki-haram; da sahihi da la’ifi duk hajarsa ce take zama hujja a kanmu?1
Kasancewar ana samun qarya da gaskiya da yawa a cikin riwayoyi, ya sa dole a koma ga ma’abuta ilimin hadisi, a matsayinsu na rariya uwar tata a fagen, don a rarrabe tsakanin garin taba da na gero. Kamar yadda ake komawa ga malaman Nahawu don banbancewa a tsakanin Nahawun larabawa da na Ajamawa. Da kuma yadda ake komawa ga malaman Lugga, don tantance abin da yake mallakar luggar da wanda ba mallakarta ba. Da kuma yadda ake tuntuvar malaman waqa da na Xibbu akan abin da ya shafe su. Kowane “Allazi” daga cikin ilimi, da nashi “Amanu” da aka san shi da shi. Wani ko “kafaru” ake samu gare shi. To, malaman Hadisi su ne mafiya girman daraja a kan sauran malamai. Su ne kuma mafiya gaskiya da xaukakar matsayi, da kishin addini.2
Gaba xayan qungiyoyin musulunci sun yarda da cewa, duk wanda ya yi imani da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama wajibi ne ya yi wa hakan rakiya da tsare dokoki. Idan kuwa ba haka ba, gobe lahira kashinsa ya bushe Annabi na ji na gani. Akwai daga cikin Shi’ah ‘yan sha biyu da ke cewa, da zaran mutum ya so sayyidina Ali Raliyallahu Anhu a zuci to, yana iya aikata duk abin da ya ga dama don ya fi qarfin zunubi. A kan haka kenan, babu wata buqata ta samun wani shugaba ma’asumi a yau, don samun wata falala, domin son da suke ma Ali Raliyallahu Anhu a cewarsu, ya ishe su shinge.3
A cikin lumana, Ibnu Taimiyyah ya warware duk shubhohin da malaman Shi’ah ke kafa hujja da su. Babu zagi babu cin mutunci. Duba waxannan maganganun nasa alal misali:
Da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi nufin naxa Ali Raliyallahu Anhu a matsayin Yarima mai jiran gado, waxannan Sahabbai uku ba zasu musa masa ba. Da kuma qaddarar Allah za ta sa su yi masa musu, da sauran Sahabbai sun shawo kansu. Don gaba xayansu ba su saba da savawa ko bari a sava wa umurnin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ba. Ba ka ganin aqalla kashi xaya cikin uku na musulmi sun tallafa ma Ali a wajen yaqar da ya yi ma Mu’awiyah alhalin ba shi da wani nassi da ya sa shi yin haka? Ya kake zato da Ali na da nassi na zama halifa tun farko, amma waxancan suka amshe masa? Nawa ne daga cikin Sahabbai za su mara masa baya a wannan hali?1
Idan ‘yan Shi’ah suka ce, Ali Raliyallahu Anhu bai tava sujada ga gunki ba, saboda ya karvi musulunci tun bai balaga ba. Kuma haka bayan ya musuluntar ma bai yi ba, tunda musulmi ne. Sai mu ce ma su, ai babu wani abin alfahari a cikin wannan. Tunda kowane musulmi haka yake. Da ma shari’a ba ta hau kan yaro ba, balle. Idan kuwa suka ce: A’a, ba muna magana ne a kan bayan musuluntarsa ba, muna yi ne kan kafin haka. To, sai mu ce masu: Wannan kuma sanin gaibu sai Allah. Mu dai ba mu san wannan magana ba. Kuma shi xan Shi’ar da ke faxar wannan magana ba ya daga cikin mutanen da ake shiga xaka da zancensu.2
Mun yafe wa xan Shi’ar qaryar ijma’i da ya yi. Muna so ya tabbatar mana da maganar ta hanya xaya ingantancciya. Domin wadda Sa’alabi ya ambata mai rauni ce. A cikinta akwai mazajen da ba a yarda da su ba. Balle daxa wanda xan magazili ya riwaito, wanda shi rauninsa ya vaci matuqa. Hadissan da ya tattara a cikin littafinsa, ko kurtu a makarantar ilimin hadisi ya san cewa qaryayyaki ne kawai aka kitsa. To, isnadin nan guda xaya rak ingantacce da muke nema gare shi muna son ya qunshe wannan magana da waccan.3
Shi dai Ibnu Taimiyyah bai tsayar da martaninsa kawai ga wannan xan taliki da yake tattaunawa da shi ba. A’a, ya fuskanci addinin Shi’ar ne ga baki xayansa ya kai masa hari da makaman hujjoji. Saurari abin da yake cewa:
Duk da yake shi wannan xan Shi’ar sawun varawo ne ya taka; ko da aka haife shi shehunansa sun riga sun yamutsa hazo a fagen tarihin musulunci. Shi kuma da ya zo sai kawai ya hau ba tare da ya tankaxe ya rairaye ba, balle ya kai ga tsagwaron gaskiyar da ma'abuta ilimi manya da qanana suka sani a yanke.4
Mawallafin ya kasance a cikin hattara sosai game da qarairayin da aka jingina ga Ali don a bajintar da shi. A irin waxannan wurare in babu cikakkiyar hattara sai a shiga rigar mutuncin Alin, wanda kuma ba shi ne manufa ba. Yi nazarin in da yake cewa:
Amma cewar da xan Shi’ar yayi Ali Raliyallahu Anhu bai tava bugun wani abu da takobinsa ba face ya gama da shi. Ba mu da masaniya akan ingancin wannan magana ko rashin ingancinta. Babu wata riwaya ingantatta a hannunmu da za mu iya rosa wannan da ita. Amma da za’a sami wani mutum shi kuma ya ce Khalidu ne da Zubairu da Bara’u xan Malik da Abu Dujanata da Abu Xalhata da makamantansu waxanda ba su tava bugun wani abu da takobinsu ba face sun gama da shi, ka ga an yi kunnen doki kenan. Musamman da yake kasancewar irin su Khalidu xin, da shi Bara’u mafi shahara da wannan irin jaruntaka kamar yadda masana tarihi za su iya faxa. Don kuwa har an riwaito cewa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Khalidu wani takobi ne daga cikin takubban Allah, wanda Allah ya zare a kan mushrikai”.
Babu wanda zai ji wani qaiqayi ko ya yi wani kokwanto, idan aka ce, wanda Manzon Allah ya siffanta da kasancewa takobin Allah, ba ya saran abu face ya gama da shi. Aka kuma taras da cewa Khalidun nan ya kashe kafirai ba adadi a fagen fama. Kuma har ya koma ga Allah bai tava gudu daga wurin yaqi ba. Wannan magana ta fi qanshin gaskiya, da an jingina ta gare shi.1
Ka ga a nan ya yi qoqarin fidda kansa ga abin da babu da tabbaci a cikinsa. A wurare da dama zaka iske ya yi irin wannan. Kamar in da mawallafin wancan littafin ya ce, wai Abubakar ya nemi a yi ma sa murabus, kuma wai, wannan ya nuna daman can shi bai cancanta ba. Sai Ibnu Taimiyyah ya ce:
Kamata ya yi marubucin ya bayyana ingancin wannan magana. Idan kuwa ba zai iya ba, to ya sani ba duk abin da aka riwaito ne gaskiya ba. Kuma saqar duk da aka kitsa a kan zance da bai inganta ba, ita ma hakan.
Abu na biyu: Idan ta tabbata cewa, Abubakar Raliyallahu Anhu ya faxi wannan magana, babu mai ikon ce masa don me? Domin kuwa babu wani dalili da zai hana a yi masa murabus xin matuqar ya nemi hakan don wani dalili na qashin kansa. Mu dai ba mu da wata masaniya a kan ya nemi murabus ko bai nema ba, balle mu ga wurin vata lokaci a kan wannan batu.2
Mawallafin ya wofintar da jimillar hajar ta ‘yan-sha-biyu, mafi yawan lokuta a cikin ruwan sanyi. Amma ya kan xan tsananta harshe a wani wurin. Kamar in da yake cewa:
A kan haka ne jahilcinsu da zaluncinsu suka gagari yawun alqalami siffantawa. Domin sun kasance suna godogo da riwayoyin qarya da ruxaxxun lafuzza da mummunan qiyasi, suna kuma ji da iqrarin cewa riwayoyi ne na gaskiya, kai mutawatirai ma. Kuma lafuzzan can nasu nassosa ne qwarara, ga su sarai. Kuma duk hujjar da suka bari ta hankali, hujja ce gar.3
Haka dai mawallafin ya ci gaba da fexe gaskiyar Allah qarara dangane da lamarinsu:
Wannan feshin qarya ba wani abu ne ba a wurin waxannan mutane, domin kuwa jini da tsokarsu da qarya suka tofo. Hakan ta sa kodayaushe suke qoqarin musanta abin da duniya ta gama tabbatar da kasancewarsa gaskiya, tare da qoqarin tabbatar da abin da duniya da lahira an yarda da kasancewarsa toka.1
Ya dai kai matsaya ta qarshe a kansu ne in da ya ce:
Babu wata qungiya ta ‘yan bidi’a da za a ce gara ‘yan-sha-biyu da su.2
Wani lokacin kuma ya kan shaci fushi don kishin kariyar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ko iyalansa da Sahabbansa daga cin mutuncin da ‘yan-sha-biyun suka yi ma su. Mafi nauyin maganar da ya furta a cikin wannan littafi ita ce maganar da ya yi a kan wautar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da ‘yan Shi’ah ke yi cewa wai, ya yi gudun hijira tare da Abubakar Raliyallahu Anhu don bai san shi maqiyinsa ne ba:
Ka ga dole ne duk wanda zai riqa a matsayin aboki a cikin irin wannan tafiya ya kasance soyayyarsa da shi ta shafe ta kowa. Hakan kuwa ta tabbata, don ya nuna masa irin baqin cikin da yake ciki a kan halin da ya shiga. Amma kuma sai duk hakan ta zama busar iska; ya kasance yana qiyayya da shi a zuci? Bayan kuma shi ya sakankance har ga Allah cewa, shi masoyinsa ne?
Ko shakka babu, babu wanda zai yi wannan zavin tumun dare sai mafi wauta da jahilcin mutane. Allah kuwa ya qasqanta duk wanda ya jingina irin wannan wauta da jahilci ga Manzonsa, kuma mafi cikar halittarsa ga hankali da ilimi da gogewa.3
Aikinmu a Cikin Wannan Littafi
Littafin da muka dogara da shi a wannan aiki shi ne taqaitaccen Minhajus Sunnah na larabci, wanda Sheikh Abdallah Al-Gunaiman, wani malami mai koyar da Tauhidi a masallacin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi. Wanda kuma aka buga shi a maxaba’ar Darus Siddiq da ke San’a’a ta qasar Yaman, a shekarar 1426H/2005M. Malamin ya bi sawun Imamuz Zahabi ne wajen taqaita littafin na Ibnu Taimiyyah akan abin da ya shafi aqidar Shi’ah ita kaxai.
A haqiqanin gaskiya ba fassara ce kaxai aikin da muka yi wa wannan littafi ba. Domin kuwa mun duba zubin littafin da tsarin tafiyarsa da kanun bayanansa duk mun yi gyara mai ma’ana a cikinsu. A wasu lokutan mukan buqaci koma ma asalin littafin na Ibnu Taimiyyah mai sifili takwas don tantance tushen maganar da yadda aka faxe ta, ko don cike wani givi da aka bari.
Game da fassara xin ita kanta, mun bi tsarin da muka saba da shi a wannan cibiya na lizimtar bayar da ma’anar magana kamar yadda mai ita ya faxe ta ba tare da qari ko ragi ba. Mukan kuma yi qoqarin kusantar da ma’anar ga mai karatun Hausa, ta hanyar lulluve ta da nau’oin adon magana da irin namu salo na Hausawa a maimakon lizimtar kalimomin da marubucin ya yi amfani kawai da su da larabci. A duk lokacin da mawallafin ya bayyana qwarewarsa a harshen larabci sai mu kuma mu bayyana tamu qwarewa a harshenmu na Hausa; sai mu haxiye maganar tasa, mu fito da ita da namu salo kamar daxai ba fassara ce muke yi ba. Wannan ita malamai suka sani da suna Fassara mai ‘yanci. Bari mu xan ba da ‘yan misalai ga masu karatu waxanda suka san harsunan biyu don gane muhimmancin bin wannan tsari da muka yi.
Ibnu Taimiyyah ya ce:
وإذا قام الدليل القطعي على ثبوت إمامتهم، لم يكن علينا أن نجيب عن الشبه المفصلة، كما أن علينا أن نجيب عما يعارضه من الشبه السوفسطائية. وليس لأحد أن يدفع ما علم يقينا بالظن.
Ga yadda muka fassara shi:
Da zarar kuwa irin wannan dalili yankakke ya tabbata, a kan dacewar halifofin da shugabancin, kamar yadda ya tabbata a wurinmu, to, babu buqatar sai mun ci dugadugan sauran qyaleqyalin da suka yi wa qaryar. Tsayawa bayar da amsa a kan waxannan wofintattun Shubuhohi, bayan an rosa ginshiqansu, vata lokaci ne. Babu wani mutum da ke iya rosa masaniyar da aka sakankance da ita, alhali makamin da ke hannunsa sungumin ragga ne kawai.1
Sai kuma in da ya ce:
الجواب من وجوه: أحدها: قد تقدم بيان بطلان كل ما دل على أنه إمام معصوم قبل الثلاثة. الثاني: أن النصوص إنما دلت على خلافة الثلاثة قبله. الثالث: أن يقال: الإجماع المعلوم حجة قطعية لا سمعية، لا سيما مع النصوص الكثيرة الموافقة له، فلو قدر ورود خبر يخالف الإجماع كان باطلا: إما لكون الرسول لم يقله، وإما لكونه لا دلالة فيه. الرابع: أنه يمتنع تعارض النص المعلوم والإجماع المعلوم، فإن كليهما حجة قطعية، والقطعيات لا يجوز تعارضها لوجوب وجود مدلولاتها، فلو تعارضت لزم الجمع بين النقيضين. وقد دل الإجماع المعلوم والنص المعلوم على خلافة الصديق رضي الله عنه وبطلان غيرهما، ونص الرافضة مما نحن نعلم كذبه بالاضطرار، وعلى كذبه أدلة كثيرة.
Ga yadda muka fassara maganar:
Mun riga mun warware duk wata magana da ke cewa, dole ne Ali ya zama halifa kafin halifofi uku da suka gabace shi. Domin kuwa gaba xayan nassosan da suka tuzgo akan shugabanci na tabbatar da halifancinsu ne kafin shi. Kuma amon ijma’i akan haka ya game duniya. Hujja ne kuma yankakka, ba naji-naji ba. Musamman kuma da aka sami nassosa da dama suka mara masa baya. Da wani labari zai tuzgo ya tunni wannan ijma’i, to, sai a tuhumce shi don ya tabbata zakka. Lalle ne kuma a qarshe a taras cewa, labarin qanzon kurege ne.
A qa’ida, ba ta yiwuwa ingantaccen nassi ya ci karo da lafiyayyen ijma’i. domin kuwa ko wanne daga cikinsu hujja ce yankakka. Su kuwa yankakkun hujjoji, amanar da ke tsattsage da cikannansu ta dalilai da ke tabbatar da ingancinsu ba ta bari su yi kabra da juna. Da wata ‘yar hayaniya za ta faru tsakaninsu sai dai a sasanta su amma ba dai rabuwa ba.2
Ga kuma wata magana tasa in da yake mayar da martani a kan wata falala da suka ce ta cancantar da Ali zama halifan farko. Ita ce wai, tauraro ya sauko qasa saboda shi. Ga abin da ya ce da larabci:
لم ينقض قط كوكب إلى الأرض بمكة ولا بالمدينة، ولا غيرهما. ولما بعث رسول الله صلى الله عليه وسلم كثر الرمي بالشهب، ومع هذا فلم ينزل كوكب إلى الأرض. وهذا ليس من الخوارق التي تعرف في العالم، بل هو من الخوارق التي لا يعرف مثلها في العالم، ولا يروي مثل هذا إلا من هو من أوقح الناس، وأجرئهم على الكذب، وأقلهم حياء ودينا. ولا يروج إلا على من هو من أجهل الناس وأحمقهم وأقلهم معرفة وعلما.
Ga yadda muka fassara ta:
Babu inda tarihi ya nuna tauraro ya tava faxowa qasa a Makka ko Madina, ko wasu garuruwa kusa da su. Eh, gaskiya ne, lokacin da aka aiko Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ana yawaita jifa da taurari. Amma duk da haka ba a samu cewa, tauraro ya tava saukowa qasa ba. Da hakan ta zama wani abu na keta hankali, kuma sananne a duniya. Hasali ma kai! Wani abu ne da bai tava faruwa a faxin duniya ba, balle ya zama abin kakabi. Kuma babu ma wanda irin wannan labari zai riqa fitowa bakinsa sai mafi wauta daga cikin mutane, wanda kuma ya ce wa musailamu cas, saboda cikar rashin kunya da wasa da addini. Kamar kuma yadda babu wanda zai saurare shi, balle har ya yarda da shi, sai mafi jahilci da wauta daga cikin mutane, wanda wayewarsa da ilimin addini ba ta cika cikin cokali ba.1
Muna fatar samar da wannan littafi a cikin harshen Hausa ya kasance babbar gudunmawa ga yunqurin da ake yi na yaxa Sunnah da warware rikittan da aka tayar a cikin tarihin magabata.
Dostları ilə paylaş: |