Rayuwar annabi


Kwaxaitar da su a kan Lailatul-qadri



Yüklə 0,65 Mb.
səhifə10/12
tarix24.10.2017
ölçüsü0,65 Mb.
#12101
1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12

4.10 Kwaxaitar da su a kan Lailatul-qadri:

Nassosan da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya kwaxaitar da Sabbansa Raliyallahu Anhum a cikin, a kan kirdado da cin moriyar Lailatul-Qdari suna da yawa. Wani lokacin yakan bayyana masu irin falalar da ke cikin daren Sallallahu Alaihi Wasallama kamar inda yake cewa: “Duk wanda ya y raya daren Lailatul-qadri da ibada yana mai cikakken imani da neman lada, Allah zai gafarta masa gaba xayan zunbbansa.” 3 Wani lokacin kuma sai kawai ya wadata da yi masu ishara da lokacin da daren zai kama a cikin watan, kamar ce masu da ya yi: “Ku kirdadi daren Lailatul-qadri a cikin kwanki goma na qarshen Ramalana.” 4

A wani lokaci kuma sai ya qara da nuna masu muhimmancin kulawa da kwannankin mara a goma na qarshen kamar cewar da ya yi: “Ku kirdadi daren Laialatul-qadri a cikin kwanakin mara na goma na qarshen Ramanala.” 5 A lokacin da kuma ya yi fargaban kasawar wasu daga cikinsu a kan tsare kwamankin goma da ibada, sai ya taqaita su a kan kulawa ta musamman da kwamnaki bakwai na qaarshen watan, inda yake cewa: “Ku nemi dacewa da Lailatul-qadri a cikin kwanaki goma na qarshe. Idan xayanku ya yi rauni ko ya kasa, to kada ya bari bakwai na qarshe su wuce shi.”6 Sannan a wani Hadisi kuma Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya tabbatar masu da cewa daren ashirin da bakwai shi ne daren, ya ce: “Duk wanda ke neman Lailatul-qadri, to ya neme ta a dare na ashirin da bakwai. Ku neme ta a cikin wannan dare”7

A kan wannan dalili ne, Ubayyu xan Ka'abatu Raliyallahu Anhu har ranysewa yakan yi a kan cewa daren ashirin da bakwai ga Ramalana shi ne daren Lailatul- qadri. Yakan ce: “Wallahi ni na san daren, shi ne daren da Manzano Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurce mu da rayawa da ibada, wato daren ashirin da bakwai ga wata.” 1 Dan Ka’abu ya yi gaskiya, domin kuwa tarihi ya tabbatar da cewa akwai shekarun da aka yi, daren na Lailatul qadri bai tavu wucewa ko kasawa daga ranar ta ashirin da bakwai ba. A wasu shekarun kuma ya koma dare na ashirin da uku. Da kuma aka xauki tsawon lokaci a haka, sai ya koma dare na ashirin da xaya.

Abu Sa’idu al-Khudri Raliyallahu Anhu ya ce, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Na yi I’tikafi a cikin kwanaki goma na farkon watan Ramalana ina lalabe daren Laitatul-qadri. Sannan na sake yi a cikin goma na tsakiya daga nan sai aka aiko mani cewa, ai daren na can cikin kwanaki goma na qarshe. Saboda haka duk wanda ke da qudurin yin I’tikafi a cikin ku, to, ya yi shi yanzu. Mai riwayar ya ci gaba da cewa: “Jin haka fa sai mutane da yawa suka shiga I’tikafi xin tare da shi Sallallahu Alaihi Wasallama. Ana cikin haka sai ya sake gaya wa mutane cewa: “Na yi mafarkin wannan dare zai kama a cikin xaya daga cikin kwanakin mara (wuturi) na waxannan kwanaki. Kuma da aka wayigari, sai ga ni ina sujada a cikin wani cava mai laka.” Mai riwaya ya ci gaba da cewa: “Safiyar ashirin da biyu ga watan na kamawa, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya fito don ya ba mu Sallar Sunahin, Sai sama'u ta kece da ruwa. Masallci ya yi Sharkaf; cavo da laka suka kankama. Ko da ya qare ba mu Sallar sai ga goshinsa da hancinsa kace-kace da laka da cavo Sallallahu Alaihi Wasallama. Sai ta tabbata cewa daren can na ashirin da xaya shi ne daren Lailatul- qadri.2

Dalilin kuma da ke tabbatar da cewa daren ashirin da uku ga wata ya yi zama na Lailataul-qadri shi ne Hadisin Abdullahi xan Unaisu Raliyallahu Anhu wanda ya ce: “Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “An nuna mani lokacin da Lailatul- qadri za ta kama, amma kuma sai aka mantar da ni. Amma ina iya tuna na gan ni ina suhada a kan cavo da laka.” Sai mai riwaya ya ci baga da cewa: “Daren ashirin da uku ga wata na kamawa ko, sai aka vare da ruwa. Manzon Allahsallallahu Alaihi Wasallama na qare ba mu Sallar Subahin ya juyo, sai ga kufan cavo da laka a kan goshinsa da hancinsa.”3 Ka ga waxannan Hadisai guda uku na qara tabbatar da gaskiyar maganar Malaman da suka tafi a kan cewa babu wanda ya san takamammar ranar da Lailatul-qadri ke kamawa a cikinta, illa dai tana ya da zango ne a cikin xaya daga cikin kwanakin wuturi (mara) na goma na qarshen watan. Wannan kuwa wani jinqayi ne da rahama daga wurin Allah, wanda sakamakonsa sai qoqarin gano daren ya yawaiya tsakanin mutane.

Bisa wannan dalili ne kuma, da irn yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya dage da raya waxannan darare da ibada, don ya dace da wannan dare, Sahabbai suka xauki hannu, su ma suka fantsama cikin kogin qoqari da ibada Ba mamaki ko kaxan idan Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da Sahabbai sun saka wannan riga. Domin kuwa Annabi, shi ne babban Malamin wannan al'umma, wanda kuma Allah ya xora mata yin koyi da shi. Shi kuma daren Lailatul-qadri kamar yadda Allah Ta'ala ya bayar da Labari a ckin Alqur’ani, dare ne da Alqur’ani mai girma ke sauka a cikinsa. Kuma ladar ibada a cikinsa ta fi ladar ibadar wata dubu. Haka kuma mala’iku da Ruhul- Qudusi na sauka a cikinsa. Kuma dare ne na salama da aminci a sakamakon yawan alheran da Allah Subhanahu Wa Ta’ala ke saukarwa a cikinsa, na gafara da afuwa ga bayanisa.

Wannan masaniya da wannan al’umma ke da ita, ta sa har a kwanukanmu na yau musulmi ke da matuqar sha’awar raya kwanaki goma na qarshen Ramalana da ibada, don su yi dace da wannan dare mai alfarma. Kuma tabbas idan Malamai suka qara zare damtse ga yi wa jama'a jagoranci a cikin raya waxannan darare da ibada, kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi, kwaxayin da mutane ke da shi a kan haka zai qara havaka. Musamman ma dai idan suka qara da lurar da su muhimmancin qaurace wa halaye da xabi’u irin waxanda ke sa Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya ba musulmi baya a cikin irin wannan lokaci mai albarka, kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya gaya mana a baya kaxan.

Duk da yake ba manufar rububa wannan littafi ba ce, yin bayani a kan I’tikafii da hanyoyin cin nasara ga mai yin sa, amma duk da haka ga wasu ‘yan shawarwari a kan haka,

1)Yana da matuqar kyau ga duk wanda ke son Li'tikafinsa ya karva sunansa, ya rage yawan wahalhalu da rana, woto ya nisanci huldoxi da gogayya da mutane barkatai. Wanda kuma bai riga ya shiga I’tikafi xin ba, amma yana tafiya Salloli, to ya riqa zuwa da wuri. Sanann gaba vayansu, su rage cin abin ci sosai. Su kuma kimtsa gida da kyau, ta hanayar tanadin duk abubuwan da iyali ke bukata, da kayan Sallah. Domin hakan za ta sa su rage yawan fitowa daga masallaci a-kai-a-kai. Ta haka sai ya kasance sun jefi tsuntsu biyu da dutse xaya. Musamman idan suka sayi kayan kafin kamawar goma na qarshen, ko ma tun kafin watan Azumin ya tsaya; sun tsere wa cunkoson mutane a kasuwanni, da farashi mai tsada, sun kuma sami cikakken lokacin ibada.

2)Haka kuma tsarkake zuciya da gavovi a wannan lokaci, daga ayyukan zunubi da savo wajibi ne, ta hanyar yin cikakkar tuba ta har abada. Wannan babban sharaxi ne, saboda cewar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: “Duk wanda ya yi Azumin watan Ramalana, ya kuma raya daren Lailatul-qadri, yana mai cikakken imani da neman lada, Allah zai gafarta masa gaba xayan zunubbansa.” 1 A wani Hadisin kuma yace: “Sallolin farilla guda biyar, da ta Juma’a zuwa Juma’a, da Azumin Ramalana zuwa wani Ralamana, suna karkare abin da ke tsakaninsu na zunubbai matuqar an nisanci kaba’irori.” 2 Ka ga a nan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayyana mana kasancewar nisantar kaba’irori sharaxin kasancewar aikin mutum karvavve a wurin Allah.

3)Lalle ne mai ibadar I’tikafi ya cika birnin zuciyarsa fal, da qaunar Allah, da ganin girmansa, da gode wa ni’imominsa tare da iya tsinkayar buwayarsa fai da voye. Haka kuma wajibi ne bawa a wannan lokaci ya yarda shi bawa ne, kuma Ubangijisa shi ne Allah. Shi. yana kuma da buqata da rahama da jinqayinsa, tare da tsananin fargaba da tsoron haxuwa da narko da azabarsa. Kuma babu wani wuri da za ya tafi ya tsere masa Subhanahu Wa Ta’ala.

Kasancewa haka wajibi ne, domin kuwa tabbataccen abu ne cewa, duk lokacin da bawa ya yi rugu-rugu ya narke gaban mahaliccinsa, bayan sanin da yake da shi na kowaye mahalicci, to a lokacin ne ayyukansa za su sami karvuwa a wurin Allah, ya sami lada ninkin-ba-ninkin. Ka da ka kusura, a matsayinka na mai neman faxa a wurin Allah ka kawai mayar da hankali ga kyautata zahirinka da inganta shi. Ka bar baxinka fanko, alhali kuwa shi ne jirgin tsira. Allah shi yi mana mawafaqa, amin.



4)Bayan wannan kuma sai mai I’tikafi ya zavi ibadar da zai neman kusanci zuwa ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala da ita a wannan lokaci. Wannan ma wajibi ne, domin kuwa ibada mataki-mataki ce. Musamman kuma a cikin wannan dare mai albarka. Abu ne mai sauqi wani ya ji cewa ibadar khushu’i da khudhuri da yin rugu-rugu tare da narkewa gaban Allah Subhanahu Wa Ta’ala ta fi kama jikinsa. Wani kuwa ya ji ba haka ba. Amma dai ala ayyi halin, duk wanda Allah ya arzutta da zurhin fahimta da ikhlasi da biyar Sunnar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, to, shi ne wanda ya fi kowa dacewa.

5)Ka da mutum ya vata lokacinsa a kan tunani da kace-nace don tabbatarwa da gane haqiqanin daren da Lailatul-qadri za ta kama a cikinsa. Abin da ya kamace shi, shi ne ya yi amfani da wannan lokaci cikin yawaita ibada. Domin babu wata lada da zai samu a cikin hakan can. Yaqn ibadar da zai tsare fai da voye ce, za ta sa ya dace da daren, ko da kuwa hakan ba ta samu ga waninsa ba. Da zarar kuwa Allah ya yi masa gam-da-katar, to ya fi wanda kakkarsa ta yanke saqa damawa.

6)Bayan duk waxannan abubuwa kuma kada ya kuskura ya xauki sauran kwanakin watan na Ramalana ba bakin komai ba, a’a. Lallai ne su ma, ya yi qoqari ya ba su wani abu na rayawa da ibada Domin kuwa ai cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: “Duk wanda ya raya watan Azumi da ibada Allah zai gafarta masa zunubansa baki xaya.” 1

Ko da muka yi wannan magana ta qarshe sane muke da cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam kansa, ya fifita kwanaki goma na qarshen Ramadana da ibada, kamar yadda Nana Aisha Raliyallahu Anha take cewa: “'Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama kan zare damtse a cikin kwanaki goma na qarshen Ramadana fiye da yadda yake yi a cikin sauran kwanaki.”1 Kai ! ko a cilin kwanaki goma na qarshe ya fifita wasu kwanaki, kamar yadda Abuzarri ke cewa a wannan Hadisi: “Mun yi Azumi tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, amma da rana xaya, bai raya dare tare da mu ba. Sai da ya rage saura kwana bakwai wata ya qare. Sannan ya kwashe sulusin dare yana Sallah tare da mu. Ranar ashirin da huxu kuma sai muka neme shi muka rasa. Sai da ana saura kwana biyar wata ya qare, sai ya fito muka yi ta Sallah har tsakiyar dare. Sai na ce : “Ya manzon Allah ! Me zai hana mu cika ladarmu? Sai ya karva mani da cewa: “Duk wanda ya yi tsayuwar dare tare da liman , bai kuma yanke ba, har sai da limamin ya yanke, to zai sami ladar wanda ya raya dare gaba xaya.”

Abuzarri ya ci gaba da cewa: “A rana ta ashirin da shida kuma sai ya yi nussan Sallallahu Alaihi Wasallam. Sai a rana ta ashirin da bakwai, ya gayyato iyali da matansa da sauran mutane, muka dinga Sallah, har sai da muka ji tsoron kada sahur ya kucce mana. Daga wannan rana kuma bai sake raya dare tare da mu ba, har watan ya qare.” 1

Sane mu ke qwarai da haka, ba kuma muna cewa ne kada a yi yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi ba. Ai bubu alherin da ya kai ga yin abu a cikin sifa da miqidarin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi. Babbar musiba, kuma abin da muke tsoro da far-gaba, shi ne a wayi gari, musamman a cikin wannan wata mai alfarma, mutane sun mayar da hankali a kan aikata haramiyya, Sun kuma manta da abubuwan da ke kansu na wajibi kamar Sallah a cikin jam’I da karatun Alqur’ani da nazarinsa. Sun manta da ayyukan zuciya, balle daxa yawaita zikiri da du’a’i da sadaqa da sauran ayyukan xa’a sun mayar da hankali ga hululu. Har a wayi gari iyakar banbancin da ke akwai tsakanin rayuwar wasu, ta sauran kwanakin shekara da ta lokacin Azumi, shi ne rashin cin abinci da rana kawai. Wannan shi ne abin da muke tsoro.

Wallahi, duk wanda ya sami kansa a cikin irin wannan yanayi, to ya yi hasara. Don ya vata lokacinsa a banza, bai bi sawun nagartattun bayi ba. Domin su, kamar yadda bayani ya gabata, da zarar watan Azumi ya kama, to sun aje komai fa kenan. Ba su da wani aiki sai Sallah da zikiri da sadaka da sauran ayyukan xa’a don neman kusanta ga Allah Maxaukakin Sarki.

Babban bala’i ma duk bai fi, watan na Ramalana ya fara ya qare mutum na haka ba. Da zarar haka ta faru, to, ya shiga sahun mutanen da Jibiru Alaihissalm ya yi wa mugun baki, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa amin, a Hadisin da ke cewa: “……Da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya xora qafarsa a kana matakar minbari ta farko sai aka ji kawai ya ce: “Amin.” Yana kuma taka ta biyu ya kuma sake cewa: “Amin.” Haka kuma ga ta uku. Mai riwaya ya ce: “Ko da ya sauko sai muka tambaye shi da cewa: “Ya Manzon Allah lafiya dai? Yau mun ji ka yi wani abu da ba mu tava ji ba.” Sai ya karva mana da cewa: “ Ai Jibirilu ne ya zo mani, yana cewa: “Allah ya la’anci duk wanda watan Azumi ya kama, har ya fita bai yi wani aiki da zai sa Allah ya gafarta masa a cikinsa ba. Ni kuwa na ce: Amin a mataki na farko. Ina isa kuma a mataki na biyu sai ya ce : “Allah ya la’anci duk wanda aka ambaci sunanka, yana kusa bai yi maka salati ba.” Na ce: Amin. Da kuma na isa mataki na uku, sai na ji ya ce: “Allah ya la’anci duk wanda ya ga tsufan iyayensa, amma bai yi masu wata hidima da za ta kai shi aljanna ba.” Nan ma na ce: Amin.” 2

To, fita batun wannan ma, akawai wasu bayin Allah da ba su damu da duk wani dare a cikin watan Ramalana, idan ba daren ashirin da bakwai ga wata ne ba. Alhali kuwa ba kodayaushe ne Lailaitul-qadri ke kamawa a cikinsa ba, a mafi ingancin zance. Duk da yake ko shakka babu, yana xaya daga cikin dararenta. Kulawar da wasu ke yi wa wannan dare ta ma wuce ta shari’a. domin a duk lokacin day a kama sai sun tafi aiki Umara. Wannan kuwa ba koyarwar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ce ba. Don bai tava kwaxaitar da al’ummarsa kan kevance daren ashirin da bakwai da aikin Umara ba. Abin da kawai ya kwaxaitar da su yi shi ne aikin Umara a cikin watan Azumi; farko ko tsakiya ko qarshensa. Babu kuma laifi a kan wannan mizani, idan mutum bai sami damar yin Umarar ba, sai daidan lokacin da wannan rana ke kamawa. Amma idan ya kevance ta da wannan ibada, to ya yi abin da Shari’aba ta umurce shi da yi ba. Bisa wannan dalili ne ka ga Sahabbai Raliyallahu Anhum ba su kevance wannan rana da aikin Umar ba. Ka kuwa san da abu ne da Shari’a ke lale marhabin da shi, babu wanda zai riga su aikata shi. Ko tunanin haka babu wanda ya tava yi a cikin su. Iyakar abin da suke yi Raliyallahu Anhum, a wannan dare mai alfarma na ashirin da bakwai ga watan na Ramalana shi ne, raya daren da sallalin nafila kamar yadda shari’a ta yi umurni. Ba kuma ma wannan daren kawai ba, haka suke yi Raliyallahu Anhum a ciki duk daren da suke kirdadon Lailatul-qadri a cikinsa. Amma kuma duk wannan sharhi da muke yi ba, ya hana kasancewar gudanar da aikin na Umara da sauran ayyakan xa’a abu mafiffici a cikin kwanaki goma na qarshen, sakamakon alfarmar watan na Azumi, ga kuma ta xakin Allah. Shi wannan wani abu ne daban. Shi kuma qoqarin aqidantar da fifikon wannan dare da wani abin da Shari’a ba ta fifita shi da shi ba, wani abu ne daban. Allah kuwa shi ne mafi sani.1

Wani nau’i kuma na irin waxannnan mutane masu shiga uku, su ne wanxanda, ba su kula da duk daren da ba wuturi ba, a cikin waxannan kwanaki goma na qarshe. Dalilinsu kuwa shi ne wai Lailatul-qadri ba ta kamawa sai a cikin wuturinsu. Wannan kuwa ko kaxan ba haka yake ba. Haqiqanin magana itace, Lailatul-qadri na iya kamawa a cikin kowane dare na kwanaki goma na qarshe Ramalana, ba sai mara ba. Domin kuwa zancen wuturi da aka yi a cikin kwankin goma na nufin a cikin kwanakin da suka gabata da waxanda suka rage. Ka ga idan aka kalli kwanakin da suka gabata, sai a nemi daren a daren rana ta ashirin da xaya da ashirin da uku, da biyar da bakwai, da kuma rana ta ashirin da tara. Idan kuma aka kalli kwanakin da suka rage, kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “A neme ta (Lailatul-qadri) idan ya rage saura kwana tara wata ya qare, ko bakwai, ko biyar ko uku.” 2 Ka ga kenan idan watan ya yi kwana talatin, kirdadon na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama zai faxa ne ba a kan kwanakin wuturi ba. Sai daren na Lailatul-qadri ya kasance a cikin shafa’i. Kenan a rana ta ashirin da biyu ne dare (kwana) tara za su rage. Bakwai kuma su rage a rana ta ashirin da huxu. Idan kuwa watan ya yi nussan, sai zancen kula da kwanukan da suka wuce ya taso.”3

Ka ga kenan babu abin da ya kamaci musulmi illa, ya nemi daren a cikin gaba xayan kwamaki goma na qarshe, kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ku kirdade ta cikin goma na qarshe´.4

Allah ya saka wa xan Mas’udu Raliyallaha Anhu da alheri, a matsayinsa na xaya daga cikin manyan Sahabbai, kuma shugaba a fagen ilimi. Wanda kuma ya qware a fagen tarbiyya da karanta Alqur’ani. Shi a nasa qoqari na tsayawa kan wannan umurni na Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam, iyakar abin da yake gaya wa almajiransa a kan sha’anin daren Lailatul-qadari shi ne, duk wanda ya raya gaba xayan darare goma na qarshe da ibada, to, ya dace da lailatul-qadari” 1

Wannan mataki da xan Mas’udu Raliyallaha Anhu ya xauka shi ne mafifici. Domin kuwa ko Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam iyakar abin da yake nufi kenan. Duk da kasance warsa mutum wanda ya fi kowa masaniya da makamar wannan dare, amma sai ya bar matsalar kife, don gudun kada mutane su yi kwance da sirdi, alhali ga lokaci, wanda suke iya cikawa da bauta ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala.

Bisa wanknan dalili ka ga kennan, babu abin da ya kamata ga Malamai da masu wa’azi, illah su dage a kan qara wa jama’a qwarin guiwa a kan qara qoqari a cikin neman kusanta ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala. Musamman acikin wannan wata mai alfarma, wanda ake hana shexanu shaqatawa a cikinsa. Inda hakan ke taimakawa ga qara bauta ga Allah, da yin bankwana da ayyukkan ashsha har abada. A qarshe kuma a koma ga Allah komawa ta har abada.

Da wannan kuma muke kira ga duk wani musulmi mai kishin addini, da fatar ganin alheri ya leqa gidan kowa, fiye da yadda hantsi ke yi, ya yi qoqarin yaxa ingantacce fiqhu da tarihin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da Sahabbansa. Musamman a kan abin da ya shafi raya daren Lailatu-qdari da ibada, don a ci moriyar da ke cikin shi. Wannan shi ne abin da ake da tsananin buqata da shi, domin kuwa daren Lailatul-qadri abu ne na daga bana sai baxi. Ga shi kuma yanzu sakarci da lalaci sun yi katutu a zukatanmu, ga lokaci kuma na qure wa. A haka kuwa wajibi a kan kowane musulmi ya nemi guzuri.1

4.11 Kyakkyawan Misali:

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a cikin wannan wata na Ramalana, ya kasance wani kyyawan misali ga Sahabbai Raliyallahu Anhum. Duk abin da yake son ya koya musu, to yakan fara ne da kansa, don da ma, doka daga gida take tashi. Su kuwa a nasu matsayi, nan da nan sai su rufa masa baya. Irin haka ta faru a abubuwa kamar haka:



  1. Buxin Baki: A wata tafiya da ya yi Sallallahu Alaihi Wasallama tare da Sahabbai, wahala ta kai masu ko ina, sai kawai ya sha ruwa bayan Sallar La’asar Sallallahu Alaihi Wasallama. Xan Abbas Raliyallahu Anha na cewa: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wata tafiya a cikin watan Ramalana bai kuma aje Azumi ba. Isarsa wani wuri da ake kira Asfan ke da wuya, sai ya ce a kawo masa qwaryar ruwa, ya sha da rana kata mutane na kallonsa. Daga nan kuma ya aje Azumin.”2 A wata riwaya kuma aka ce cewa ya yi: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wata tafiya a cikin shekarar da aka ci Makka da yaqi, kuma a cikin watan Ramana, yana kuma xauke da Azumi, Da isarsa Asfan sai ya nemi a kawo masa qwaryar ruwa da rana kata, don Sahabbai su ganar wa idonsu. Aka kawo ya sha, ya kuma aje Azumin tun daga lokacin, har zuwa lokacin da ya ci Makka da yaqi a cikin watan na Ramalana.” Bisa wannan dalili ne shi xan Abbas Raliyallahu Anhu yake cewa a nasa fikhu: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi Azumi a lokacin tafiya, ya kuma sha. Saboda haka idan mutam ya ga dama ya yi Azumi, idan yana cikin halin tafiya. Idan kuma ya ga dama yana iya ajewa.”1

Shi kuwa Jabiru Raliyallahu Anhu a nasa Hadisi, a kan wannan mas’ala cewa yake yi: “Manzon Allah yana xauke da Azumi. Ko da aka kai wani wuri tare da shi, wasu a qasa wasu kuma a kan ababen hawa, suka sami kansu a cikin mawuyacin hali saboda Azumi. Har wani daga cikin Sahabbai ya kai ga ce masa: “Ya Manzon Allah! Azumin nan fa ya kai wa wasu mutane ko ina. Jira kawai suke yi su ga matakin da za ka xauka.” Nan take, in ji Jabiru Raliyallahu Anhu sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi umurni da a kawo masa qwaryar ruwa, ya xaga ta sama kowa ya gani ya kuma sha Sallallahu Alaihi Wasallama. Ganin haka sai wasu suka aje Azumin, wasu kuma suka qi ajewa. Da labari ya kai kunnensa Sallallahu Alaihi Wasallama cewa wasu fa ba su aje Azumin ba, sai ya ce: “Ai ko sun yi laifi.” 2

Wata riwaya kuma cewa take yi: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wata tafiya a cikin watan Azumi. Sai Azumi ya galabaitar da xaya daga cikin mutanen da ke tare da shi, har ya tilasta taguwarsa bibiyar inuwar itace. Da aka tababta wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sai ya umurce shi da aje Azumi. Daga nan shi ma Sallallahu Alaihi Wasallama sai ya nemi a kawo masa qwaryar ruwa, ya sha mutane na ganin haka sai suma suka sha.”3



(ii) Sallar Dare: Wani lokaci a cikin watan Azumi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita a tsakar dare ya nufi masallci don yin qiyamullaili, wanda hakan ta zama wata koyarwa da kyayyawan misali ga Sahabbai Raliyallahu Anhu. Nana Aisha Raliyallahu Anha ta riwaito cewa: “Wata rana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita bayan dare ya tsala, ya nufi masallaci don ya yi Sallah. Yana fara Sallar kuwa ashe wasu Sahabbai suna ganin sa, sai kuwa suka bi shi.”4

(iii) I’tikafi: Irin haka ce ta faru a Li'tikaf, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya shige shi don neman dacewa da daren Lailatul-Qadri, ya kuma kwaxaitar da Sahabbansa Raliyallahu Anhum a kan haka. Abu Sai’d Al-Khudri Raliyallahu Anhu na cewa a wani Hadisi: “Haqiqi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi I’tikafi a cikin kwanaki goma na farkon Ramalana, sannan ya sake yi a cikin goma na tsakiya, a cikin wata hema irin ta Turkawa, wadda aka yi wa labule da wata qiren tabarma. Sai kawai muka taru a jikin hemar, sai kawai muka ga ya kama tabarmar da hannunsa, ya kuma turo kansa waje, ya nemi mutane su matso. Sai ya ce: “Na yi I’tikafi a cikin goma na farko ina neman wannan dare. Sannan kuma na sake yi a cikin goma na tsakiya. To, an gaya mani cewa daren yana kamawa ne a cikin kwanaki goma na qarshen watan. Saboda haka duk wanda ke da niyyar yin I’tikafi daga cikinku, to ya shige shi yanzu.” Qarshe kuwa sai mutane suka shiga ibadar tare da shi Sallallahu Alaihi Wasallama.5 Haka kuma Nana Aisha Raliyallahu Anha na cewa: “Mnazon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya buga wa Sahabbai kyakkyawan misali, ta hanyar shiga I’tikafi a cikin kwanaki goma na qarshen Ramalana, ya kuma gaya masu cewa: “Ku kirdadi Lailatul-Qadri a cikin goma na qarshen Ramalana.” 1

Muhimmancin koyarwa ta hanyar farawa da kai, wata babar hanya ce da kyakkaywan misali. Yana da wuya matuqa duk da yake abu ne mai sauqi qwarai da gaske ga liman ko wani Malami ya shirya wata huxuba a ka, ko a rubuce, mai kyau da matuqar qayatarwa, amma ba za ta sami ratsa zukatan masu saurare ba, kamar irn yadda za ta yi idan da ma idanunsu sun daxe da ganin Malamin na aikata abin, ko kuma yanzu yake aukata shi tare da gargaxin. Sakankancewa da gaskiyar wannan Magana ne ya sa Hasanul-Basari saten wata kuyangaya 'yanta, kafin ya yi wa mutane gargaxi da su ‘yanta bayin da ke qarqashin su, kamar yadda wasu bayi suka nemi alfarmar ya yi. Nan da nan kuwa ganin haka, sai mutane suka karva gargaxin nasa, suka yi ta 'yanta bayinsu.

Bisa waxannan dalilai, ko shakka babu matuqar musulmi na fatar ganin alheri da ihsani sun cika wannan al'umma, to lalle ne maganganunsa su tafi kafaxa-da-kafaxa da ayyukansa. Kuma da haka ne kawai za iya kauce wa faxawa cikin sahun waxanda Allah Ta'ala ke ce wa: “Ya ku waxanda suka yi imani! Don me kuke faxin abin da ba ku aikatawa? (61:2) Muna roqon Allah Ta’ala, ya yi mana arziqin riqo da addinsa, da yin kira a ckin hikima zuwa ga biyar shari’arsa da nisantar sava masa, amin.

Da wannan muna iya fahimtar cewa farawa da gabatar da kyakkyawan misali ga mutane kafin kiran su zuwa ga wani abu, wani babban ginshiqi ne, da kuma sharaxi na cin nasara ga masu wa’azi da garagaxi. Domin kuwa sai ta wannan hanya ne za a iya zaburar da bayin Allah da kyau, su tashi tsaye, ba ji ba gani su kama ayyukan alheri. Hakan kuwa tana faruwa ne, saboda qwaqwalansu sun riga sun wasu sun kuma fahimci abin da ake nufi cikin sauqi. Ta yadda ko sun ce ba su gane ba hankalin masu hankali ba zai karva ba. Saboda haka ne Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama yake ba irin wannan salo na koyarwa matuqar muhimmaci, tare da kwaxaitar da Sahabbansa a kan duk wani saqo da za su isar daga gare shi, to su isar da shi ta wannan hanya. Dole sai da haka, domin kuwa fahimtar irin rawar da wannan salon isar da saqo ke takawa ne, da maqiyan wannan al’umma tamu suka yi, suka cika gidajenmu da miyagun darussa ta hanyoyi da na’urori daban-daban, ta yadda ba za mu iya hana su ba.

Eh ba za mu iya ba mana, matuqar ba shirye Malamanmu suke ba, da komawa su yi wa tarihin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama da na managarta daga cikin magabata, da gaba xayan tarihin nasarorin wannan al’umma nazarin qwaqaf ba. Su fito da abubawan da ke kimshe cikinsu na kyakkyawan misalai da kyakkyawar siga. Na farko ke nan.

Abu na biyu kuma, idan sun amince da yin wannan jan aiki, wajibi ne kuma a kansu, su zama waxanda ake iya buga misali da su a zamanance, a matsayin waxanda ke wakiltar Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama. Ta wannan hanya ne kawai, za a iya karya lagon varna, a kuma qara wa musulmi imani da sakankancewa da cewa har gobe, musulunci na iya takalihin xan Adamu, don ga shi suna gani a zahiri yana aikinsa.

Duk da yake a tantagaryar gaskiya, ba nagartantun Malami ne babu ba, masu iya bayar da wannan kyakkyawan misali. A’a, akwai su Alhamdu lillahi, duk da yake sun yi qaranci idan aka yi la’akari da irin yadda ake da su ko ina a da can. Ba a nan matsalar take ba. A’a matslar ita ce rashin iko, wato rundunar shexan a yau, wadda ta mallaki duban hanyoyi na qere-qere da nau’rorin zamani, na kallace-kallace da maganganu da rubuce-rubuce, waxanda suka cika duniya fal, sun ribance hankalin mafi yawan al’umma, ta yadda ko sauraren waxannan limamai ba su yi, balle kallon su. Saboda haka ka ga kenan aikin ba xan qarami ba ne, godaben ne maia tsawo sosai. Naxe shi da tafiya sai ya ci xinbin rayuka da lokaci da dukiya. Dole sai an sami gwarajen mutane, waxanda za su yi arkawali da Allah, su kuma cika, ta hanayar xaukar wa kansu wannan nauyi, suna masu kafewa sosai, tare da fata da neman yardar Allah Maxaukakin Sarki.

Musulmi, za mu iya cin wannan nasara idan muka yi amfani da watan Azumi. Lokacinsa babbar dama ce da za a iya xora harsashen wannan aiki. Saboda da ma shexanu a cikinsa ba su da wata walwala; an yi masu ququmi. Kuma zukatan musulmi a wanna lokaci shirye suke da karvar gaskiya. Wani babban al’amari kuma shi ne, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya bar mana gadon hikimomi da salailai daban-daban na yadda ake iya gina al’umma ta gari a cikin sauqi da nasara.

Muna roqon Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya yi mana mawafaqa da yi masa xa’a, tare da nisantar savonsa. Ya sa mu zama sanadin alheri a kodayaushe, ba sharri ba, amin.



4.12 Tausaya Masu:

A fili take cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na tausaya wa Sahabba Raliyallahu Anhum, kamar yadda tarihin rayuwarsa ya nuna. Kuma wannan ba abin mamaki ne ba, domin kuwa da ma can Allah Subhanahu Wa Ta’ala bai aiko shi ba, sai don ya zama rahama ga mutane baki xaya, kamar yadda yake cewa Subhanahu Wa Ta’ala:Kuma ba mu aiko ka ba face domin wata rahama ga talikai.” (21:107) Shi kuma Manzon Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ba a aiko ni don komai ba, face don in zama rahama (ga mutane).” 1 Ta kuwa tabbata, domin rahama da jinqayinsa sun zama ruwa dare game duniya,Sallallahu Alaihi Wasallama.

Dangane da abin da ya shafi rahama tsakaninsa Sallallahu Alaihi Wasallama da Sahabbansa, musammana a lokacin watana Ramalana, abubuwa kamar haka, na iya isa dalili:

1) Aje Azumi: Ta tabbata cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a lokacin wata tafiya, ya aje Azumi don tausaya wa ga Sahabbansa Raliyallahu Anhum tattare da ba ya da buqata da hakan:

Abu Sa’id Al-Khudri Raliyallahu Anhu ya ce: “Wata rana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cikin halin tafiya tare da Sahabbansa Raliyallahu Anhum a cikin wani yini mai tsananin zafin rana, suna kuma duk xauke da Azumi. Ga shi kuma su qasa suke tafiya, amma shi a kan taguwarsa ya ke Sallallahu Alaihi Wasallama. A haka sai suka iso wurin wani tafki. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi masu umurni da su sha, wato su aje Azumi. Sai suka nuna masa tun da shi bai aje ba to sun fi son su ci gaba da Azumin tare da shi. Sai ya ce ba xaya muke ba. Na kuma fi ku sauqi tunda a kan dabba nake. Suka dai dage. Daga nan Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya dafa katattararsa ya sauko ya sha ruwan, sai su kuma suka sha. Amma tabbas shi, bai yi nufin sha ba Sallallahu Alaihi Wasallama.1

2) Saurara wa Azumi: A wata tafiyar kuma Annabi Sallallahu Alaih Wasallama ya umurci Sahabban nasa Raliyallahu Anhum da saurara wa yin Azumi, saboda tausayawa gare su, ganin sun kusa yin gum da maqiya.

Abubakar xan Abdurrahman ya riwaito daga bakin wasu Sahabbai, ya ce: “Na shaidi lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci mutane da saurara wa Azumi a lokacin wata tafiya; shekarrar da aka ci Makka, yana mai ce masu: “….don ku ji qarfin haxuwa da maqiyanku.” Amma fa shi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai aje Azumin ba.”2



3.) Hana su Yin Xoreri : Saboda tsananin tausayi ga Sahabbai, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya hana su yin xoreri, tattare da shi yana yi.

Nana Aisha Raliyallahu Anha ta ce: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya hana Sahabbai yin xoreri don tausyawa gare su. Sai suka ce masa: “To ai kai kana yi.” Sai ya karva masu da cewa: “Ai ba halittarmu xaya da ku ba, Ni Ubngijina yana ciyar da ni.”3



4.) Kwaxaitar da su Gaggauta Buxin Baki da Yin Sahur: Haka ta tabbata a bakin Sahlu xan Sa’ad Raliyallahu Anhu wanda ya ce: “Haqiqa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Matane ba za su gushe cikin alheri ba, matuqar suna gaggauta buxin baki.”4

Haka kuma Irbadhi xan Sariyata Raliyallahu Anhu ya ce: “Na ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na gayyatar Sahabbai cin abincin Sahur a cikin watan Azumi yana cewa: “Ku yo sauri kada abincin ga mai albarka ya qare.5



5.) Barin Qiyamul-Laili Tare da Su: Kamar yadda bayani ya gabata, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi haka ne don tausayawa ga Sahabbai Raliyallahu Anhum kada a wajabta wannan Sallah a kansu. Ya kuwa san idan abin ya zama haka, to al’ummarsa za ta wahala.

Nana Aisha Raliyallahu Anha na cewa: “Wata rana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tafi masallaci don yin qiyamullaili, wasu mutane (Sahabbai) suka bi shi. Da ya dawo gobe, sai suka qara yawa. A dare na uku, ina ji, ko na huxu, sai jama’a suka taru maqil suna jiran ya fito, shi kuwa sai ya yi nussan. Da gari ya waye, sai ya yanki hanzari gare su yana mai cewa: “Na ga ai irin yadda kuka taru jiya, kuma ba komai ya hana ni fitowa ba, sai gudun a wajabta Sallar a kanku.” Wannan, inji mai riwayar, ya faru ne a cikin watan Azumi.1



6.) Sassauta Sallah: Ta tabbata cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan sassauta Sallah a duk lokacin da yake yin ta tare da Sahabbai a matsayin liman.

Anas Raliyallahu Anhau ya ce: “Wata rana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana Sallah a cikin watan Azumi, sai na zo na tsaya gefensa na bi. Can kuma wani mutum ya zo ya tsaya tare da ni. Haka dai har muka yi yawa. Da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya fahimci muna bayansa sai ya ci gaba yana sassauta Sallar. Da ya koma cikin gida, sai ya ci gaba da Sallarsa, ba irin wadda ya yi tare da mu ba. Da safiya ta waye sai muka tambaye shi, halama daren jiya, ya fahimci muna bayansa? Sai ya karva mana da cewa: “Tabbas na fahimci haka, ai a kan haka ma ne na yi abin da na yi.2

Babban abin da ya kamata a fahimta a cikin wannan lamari shi ne, wannan jinqayi da tausayi da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke da su zuwa ga al’ummar sa, cuxanye suke da so da qauna da girmamawa. Kuma a sanadiyar haka ne ma, yakan bar ra’ayinsa a wasu lokuta, ya koma ga nasu a aikace, idan maganar fatar baka ta kasa biyan buqata. Yana kamata matuqar gaske, Malamai da masu da’awa su yi koyi da wannan kyakkyawar xabi’a ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, kai su ma mayar da ita aqida. Rungumar wannan xabi’a kusan wajibi ma ne a kansu Domin kuwa la’akari da raunin da matane suke da shi, tare da tausaya masu a kai, ta hanyar qin wajabta masu abin da mutane ke iya wajabatawa kansa, na mustahabbi da ake nufi cikin sauqi. Abokin tafiyar wannan salo, shi ne tafiya da su mataki-mataki har a qure maleji. Hakan kuwa shi ne babban mabuxin zuciya wanda ke cika ta da fara’a da yarda tare da miqa wuya zuwa ga tafarkin shiriya da tsira.

Ya Ubangiji ma’abucin girma da xaukaka, ka sa mu gane addininka, mu zama masu tausaya wa halittunka, masu hikima a cikin kira zuwa ga dokokinka, amin.



4.13 Ba su Kariya:

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama a wannan lokaci na Ramana kamar sauran kwanukan shekara, yakan ba Sahabbai cikakkar kariya, don gudun kada shexan ya saka su cikin waswasi da mummunan zato. A lokaci xaya kuma a irin wannan yanayi, shi kansa hakan kan zama wata kariya gare shi daga zama sanadin qaiqayi a zukatan wasu.

Sayyida Safiyya Raliyallahu Anha ta ce: “Na kai wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ziyara a cikin wani dare yana I’tikafi. Da na qare maganar da nake yi da shi sai na tashi don in koma. Sai shi kuma ya taso don ya yi mani raqqiya.” Mai riwayar ya ce: “Dakinta kuwa a lokacin yana cikin gidan Usamatu xan zaidu ne. Ana cikin haka sai ga wasu Ansaru guda biyu sun biyo hanyar. Suna ganin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sai suka qara sauri. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masu: “Ku daina sauri, ai Safiyyyatu ce ‘yar Huyayyu.” Yin haka su kuma sai suka ce: “Subhanallah! Ya Manzon Allah ai abin bai kai can ba.” Sai shi kuma ya ce: “A’a, ai shexan da kuke gani yana yawo cikin jikin mutam ne kamar yadda jini ke yawo cikinsa. To ina tsoron ya jefa wani mummunana zato a cikin zukatanku, ko dai wani abu.”1

Malam xan Hajar ya ce: “Akwai fa’iadoji da dama a cikin wannan Hadisi. Na farko ya nuna mana yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke ji da al’ummarsa, da irin yadda yake xora su a kan tafarkin kaucewa daga faxawa cikin zunubi. Na biyu kuma ya nuna mana yadda shi Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi qoqarin kare kansa daga zama abin yi wa mummunan zato, balle shexan ya yi murna, shi kuma ya koma yana yankan hanzari da neman mafita. A kan haka ne Malam xan Daqiqul-Idi ya ce: “Koyi da irin wannan xabi’a ta Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya zama wajibi a kan Malamai da almajiransu. Ba ya halatta gare su, su aikata duk abin da zai sa a yi masu mummunan zato, ko da kuwa suna da hujja a wurin Allah a kan haka. Saboda hakan za ta sa a daina sauraren su, balle a amfana da ilimin da Allah ya ba su.”2

Wannan wajabaci yana qara qamari musamman, a wannan zamani namu da masu suka da neman ganin Malamai da masu wa’azi sun xan yi vatan kai, suka yawaita. Irin waxannan mutane na nan ko’ina. Sun wasa takubban halsunansu, sun tattara kalmomi da jimlolin qarya, jira xai suke yi wata talalaviya ta kwashi wani Malami, su kuwa, su yi masa ambush. A irin wannan yanayi, tabbas ya zama wajibi ga masu da’awa su qare kaffa kaffa. Yin kunne uwar shegu da wannan gargaxi ko alama ba zai haifa wa wannan al’umma xa mai ido ba. Masammam idan aka yi la’akari da irin yadda rubabi-rubabin malamai, waxanda bas u iya bayar da gamsassun amsoshi ga masu ‘yan jaye-jaye ba, suka yawaita. Irin waxannan Malamai, ko kansu ba su iya kore wa quda balle almajiransu.

Ya kamata mu fahimci cewa kariyar mutunci da masu da’awa za su yi wa kansu, na matuqar alkintawa da xaga alqadarin da’awar ita kanta. Ta yadda ba sai sun yi wahalar ba ta kariya ba. Allah shi yi mana mawafaqa, amin.



4.14 Cuxanya da su:

Babu wani lokaci da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya qyamaci Sahabbansa, balle ya guje su. Su ne abokan zamnsa kodayaushe, kuma abokan kaiwa da kowkwarsa. Haka abin yake ko a cikin wannan wata na Ramalana mai alfarma.

Baya kaxan mun ji cewa Shaddadu xan Ausa Raliyallahu Anhu ya ce: “Wata rana sha tara ga watan Azumi, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na riqe da hannuna, har muka iso wani wuri da ake kira Baqi’u, inda muka taras da wani mutum ana yi masa tsaga. Sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Azumin wanda ake yi wa tsaga da na wanda ke yi sun vaci.”3 Haka kuma Abdullahi xan Harisata Raliyallahu Anhu ya riwaito daga bakin wani Sahabi na Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama wanda ya ce: “Na shiga wurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama na taras yana sahur sai ya ce: “Matso mana mu ci, abinci ne da Allah ya sanya mana albarka a cikinsa.1 Sai kuma Hadisin Zaidu xan Sabitu Raliyallahu Anhu inda yake cewa: “Mun ci abincin sahur; hannunmu hannun Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama, sannan ya miqe don shirin Sallah sai na ce masa: “Tsawon kamar minti nawa ya kamata mutum ya sanya tsaknin sahur da kiran Sallah? Sai ya karva mani da cewa: “Gwargwadon abin da za a iya karanta aya hamsin a cikinsa.”2

Bayan wannan kuma Irbadhi xan Sariyata Raliyallahu Anhu ya ce: “Na ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yana yekuwar a zo a ci abincin sahur tare da shi a wani dare na Ramalana, yana cewa: “Ku zo mu ci abincin ga da Allah ya sanya albarka a cikinsa.”3 Shi ma Hadisin da Abu Harairata ya riwaito inda yake cewa: “Wata rana muna zaune awurin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama sai ga wani mutum aguje ya zo wurinsa. Yana mai cewa: “Ya manzon Allah! Na halaka.” Annabi ya ce masa: “Lafiya, ya aka yi ne?” Sai ya karva masa da cewa: Na abka wa matata ne ina kuma xauke da Azumi.”4

Bisa wannan asasi, ya zama wajibi a kan duk wani mai da’awa, ya riqa cuxanya da mutane. Domin sai da haka ne buqatarsa, ta su shiriya za ta biya. Ba kawai cuxayar ce da su ake murdi ba, a’a. Abin da take samarwa na kyakkyawar fahimta, faxaka da gane makamar addini, xabi’u na gari da sauran abubuwa masu kama da wannna ne abin raji. Ba ana buqatar ne tare da cuxanyar tasu ta zama kamar ta kowa da kowa ba. A duk lokacin da vata lokaci da hirace hiracen banza da wofi da sharholiya, tare da aikata abubuwa da ba su da amfani duniya da Lahira ne, za su biyo bayan cuxanya, to buqata ba ta biya ba.

Yana kuma da kyau mai da’awa ya zavi wasu lokata don wannan cuxanya, kada abin ya zama kullum, don gudun kada qimarsa ta rage a idanunsu, qarshe a yi ba tulu ba ruwan daxi. Saboda wannan manufa ne shugaban masu da’awa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke qiyamullaili da I’tikafi a kowace shekara cikin watan Ramalana. Wannan kuwa wajibi ne, domin ba mutane hutu, ta hanyar qaurace masu na xan wani lokaci, na taimakawa ga sabanta nishaxi da dawowa da rayuwa cikin hayyacinta, tare da kwakkwafe ta cif. Saboda haka sai mu yi hattara. Allah ya sa mu dace, amin.



4.15 Karvar Baqi:

Hidimar Azumi da nauye-nauyensa, ba su hana Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama karvar baqi na kusa da na nesa ba, har ma ya yi masu hidima.

Ibn Ishaq na cewa: “A cikin wannan wata na Ramalana ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya baro Tabuka ya iso Madina. A daidai lokacin ne kuma baqi, wakililan mutanen Saqifah suka zo wurinsa.”5 Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sa aka kafa masu hema a cikin farfajiyar masallaci, don ya sanyaya zukatansu:1 Ya kuma xauki nauyin aika masu da abin ci har can.2 Bayan sun karvi Musulunci sai suka ci gaba da Azumi tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama har wata ya qare. A tsawon wannna lokaci, yakan tafi wurinsu kowane dare bayan Sallar Isha’i ya yi masu wa’azi tare da laqanta masu makamar Addini.3 Bayan haka sai kuma ya umurci Usmanu xan Asi Raliyallahu Anhu ya riqa ba su Sallah. Shi ne mafi qarancin shekaru a cikinsu, amma kuma duk ya fi su hazaqar koyon karatun Alqur’ani da sanin makamar addini. Bayan ya xora masa wannan nauyi Sallallahu Alaihi Wasallama. Sai kuma ya yi masa wasiyya da cewa: “To idan fa aka sa mutum limanci wa mutane, so ake yi ya sassabta, domin kuwa a cikin su ba a rasa mai rauni, da maras lafiya, da tsoho, da mai wata buqata. Amma idan za ka yi Sallah kai kaxai, to kana iya yin duk yadda kake so.”4 Daga cikin waxannan mutane akwai mai ciwon kutarta, shi kam, sai Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya aika masa da cewa, a gaya masa: “Mun karva mubaya’arsa, ba sai ya iso ba.”5 Haka kuma an riwaito cewa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan saura’ri waxannan baqi nasa har ma su yi masa tambaya ya karva, duk a wannnan lokaci. Kamar yadda Jabir Raliyallahu Anhau yake cewa: “Tabbas wakilan na mutanen Saqifa sun yi wa Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama tambaya wata rana da cewa: “Ya Manzon Allah! Ya za mu yi da matsalar wanka idan ya kama mu domin qasarmu qasa ce mai tsananin zafi.?” Sai ya karva masu da cewa: “Ni kam nakan zuba ruwa ne har sau uku a kaina.6

Wannan qoqari da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ke yi na cuxanya da mutane a cikin watan Azumi, da karvar manya da qananan baki, waxanda ke tahowa don karvar Musulunci ko fatawa daga gare shi. Duk waxanan qoqarce-qoqarce wani nau’i ne na dabarun kira zuwa ga addini Allah, irin wanda mafi yawa daga cikin masu da’awa, da tutiyyar riqo da Sunnah, ba su cika kula da shi ba. Musamman irin waxanda yanayin aiki ko matsayin da suke da shi na ilimi ya sa tilas sai sun yi hulxa da jama’a. Ka kuwa san duk wanda ya kasance haka, lalle ne akwai buqatar ya zama mai yawan haquri da karimci da xiyauci, ta hanyar sadaukantar da ilimi da lokaci da har mutuncisa.

Duk wanda Allah Ta’ala ya jarraba da zama haka, ba makawa gare shi illa ya yi qoqarin gudanar da rayuwar nan tasa kamar yadda Shari’a ta shata. Ta hanyar shiga jama’a da damuwa da al’amuransu, tare da bayar da kowace irin gudunmawa ga abin da zai kawo ci gabansu.

4.16 Tsawatawa:

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama kan tsawata wa sahabbansa, ta hanyar nuna rashin amincewarsa da duk wani abin da suka kasa daidaituwa a kai. Wani lokaci ma har wasu ‘yan manyan kalmomi masu nuna rashin yarda yakan furta Sallallahu Alaihi Wasallama.

A baya kaxan Jabiru xan Abdullahi ya gaya mana a wani Hadisi cewa: “Wata rana a cikin watan Azumi na shekarar da aka ci Makka da yaqi, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya fita tare da Sahabbai, suna kuma xauke da Azumi har shi. Isarsu wani wuri da ake kira Kira’ul Gumaimu, sai ya yi umurni da a kawo masa qwaryar ruwa. Ya xaga ta sama kowa ya gani sannan ya sha. Daga baya sai labari ya zo masa cewa, wasu Sahabbai fa wannan bai sa suka aje Azumi ba. Sai ya ce Sallallahu Alaihi Wasallama: “Lalle waxannnan masu laifi ne, masu lalifi ne.”1

Abin da ake iya fhimta a cikin wannan magana shi ne Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya qyamaci Azumin da waxannan Sahabbai suka ci baga da shi, ba don yin haka bai halasta a Shara’a ba, asalatan. A’a, ya yi haka ne Sallallahu Alaihi Wasallama a dililin xayan abubuwa biyu. Ko dai saboda sun zama saniyar ware. Wato wani abu da ke sharxanta aje Azumi ya kama amma sun qi ajewa. Ko kuma saboda irin wahalar da suka haxu da ita cikin tafiya.2

Babu wata matsala a cikin wannan mas’ala, balle a mayar da hankali kacokwam a kanta. Abin da ya wajaba a kan kowane musulmi shi ne qoqarin yaxawa da yayata alleri, tare da tsarkake watan na Azumi daga miyyagun xabi’u, domin kuwa abin ya vaci. Varnace-varnace da wasu ke yi a cikin wannan wata mai alfarma, abin ya fi qarfin a kira shi kuskure sai dai ganganci.

Wajibi ne musulmi duk ya yaqi irin waxannan abubuwa, ya yi fito na fito da su, musammam a gida da wurin aikinsa, don koyi da cewar da Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: “Duk wanda ya ga abin qi daga cikin ku, to ya hana shi da hannunsa. Idan kuma hakan ta faskara. To ya yi amfani da harshensa. Idan kuma haka ta faskara, to sai ya qyamaci abin a zuci. Amma fa wannan shi ne mafi raunin imani.3



4.16.1 Kaffa-Kaffa da Imanisu:

Yin kaffa- kaffa da imanin mabiya don gudun ya salwanta wajibi a kan kowane magabaci mai hikima da hangen nesa. Ta tabba cewa Annabi Sallahu Alaihi Wasallam kan yi amafani da wannan salo da dama a wasu lokuta, a cikin watan Azumin Ramala, a kan Sahabbai. Hakan kuwa koyarwa ce da darasi ga sauran al’ummarsa.

Hadisi ya zo da bayanin cewa Umar xan Abu Salmata Raliyallahu Anhu ya tambayi Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallama cewa: “Ko ya halasta mai Azumi ya sumbanci iyalinsa?” Sai ya karva masa da cewa: “Tambaya wannan,” wato Ummu Salmata. Fuskantar da wannan tambaya gare ta ka da wuya, sai ta karva masa da cewa: “Manzon Allah kan yi.” Daga nan sai Umar xin ya fuskanci Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallama da cewa: “Ya manzon Allah! To ai kai Allah ya riga ya gafarta maka laifukanka auwalan wa ahiran.” Sai Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam ya qara shi gaba da cewa: “Bayan haka kuma, wallahi babu wanda ya kai ni tsora da kiyaye dokokin Ubangiji daga cikin ku. 1 (Yana nufin kar su biye masa a nan).

Haka kuma an riwaito Abu Hurairata Raliyallahu Anhu na cewa: “Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallama ya yi hani daga yin xoreri. Sai wani mutm daga cikin musulmi ya ce: “Ya manzon Allah! To ai kai mun ga kana yi, ya kenan.? Sai ya karva masa Sallahu Alaihi Wasallam da cewa: “Ai kafaxarku ba daidai take da tawa ba, domin kuwa ni, a cikin dare Ubangijina na xauke mani lalurar yunwa da qishirwa.” Wannan magana ba ta sa waxannan mutane suka tsaya matsayinsu, suka nisanci xoreri ba. Ganin haka Annabi Sallahu Alaihi Wasallam don ya tabbatar masu da cewa hanyar jirgi daban ta mota kuma daban, sai ya ci gaba yana xoreri, suna biye da shi. A rana ta uku sai ga wata ya tsaya. Domin Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam ya nuna masu cewa ya yi hakan can ne, don su gane kuskurensu sai ya ce masu: “Da Allah bai sa wata ya tsaya ba da na qara na uku a xore.”2

Shi kuwa Anas Raliyallahu Anhu, a kan wannan magana ta xoreri, cewa ya yi a nasa Hadisi: “….. Da ma a qarshe watan Azumi ne wannan al’amari ya faru. Ganin Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam ya kama xoreri ba ji ba gani, sai wasu daga cikin Sahabbai suka rufa masa baya. Ganin haka sai ya yi masu kandako da cewa: “Me ke faruwa na ga wasu daga cikinku suna xoreri? Ku tuna fa matsayina da naku ba xaya ba ne? Amma sa’a kuka yi watan ya qare. Da kwanansa ba su qare ba, lalle da idan na sullata ina Azumi ba ajewa, sai masu son zurfafawa daga cikinku sun yi saranda sun ba ni gari.3

Wannan matsayin da mataki da Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam ya xauka na nuna wa musulmi cewa Shari’ar Musulunci, Shari’a ce da ba ta son ta shaqe wa mabiyanta zaiti, kamar yadda kuma yake yi mana hannuka mai sanda da cewa: “Duk wanda ya yi wa addinin Musulunci kwasar karan mahaukacciya, lalle kuwa sai wankin hula ya kai shi dare.” 4 Nassosa da dama da ke qunshe da irin wannan ma’ana mai nuna cewa sauqi da kore matsuwa, da nisantar tsananta wa rai, su ne ginshiqin wannan addini. Su kuwa waxannan tanade-tanade da Allah Maxaukakin Sarki ya yi wa wannan addini ado da qawanya da su, na dacewarsa da xabi’ar xan Adamu ta asali, tarihi ya tabbatar da cewa da hakan ne addinin ya sami gindin zama da wanzuwa har abada. Godiya kuwa ta tabbata ga Allah, wanda ya ni’inta mu da wannan addini na Musulunci.

Haka shi ma wancan horo da Annabi Sallahu Alaihi Wasallam ya yi wa waxancan Sahabbai masu kyakkyawar niyya da son koyi da shi, abu ne da ya yi dai-dai. Domin ya dace da xabi’ar xan Adam. Wato a lokacin da ya gudar masu wahala da shiga uku Sallahu Alaihi Wasallam, amma wasu daga cikinsu suka kasa fahimta. A irin wannan hali ya yi wani abin da zai sa su jiya a jikinsu, tun da Allah a cikin ikonsa bai yarda kunnuwansu suka ji ba. Wani abin lura kuma a nan shi ne, kai ka san ba don abin da suka yi na haramiyya ba, ya yi masu wancan hora Sallahu Alaihi Wasallam. Don da haka ne kai ka san ba za su ko kusance ta ba. Shi kuma ba zai tava masu a kan ta ba. Amma kasancewar al’amarin halas, sai ya sakar masu gatari ya riqe masu votar, tunda sun ce suna iya haxiyewa. Ya kuma yi masu haka ne Sallahu Alaihi Wasallam kamar yadda muka faxa a baya, don ya tabbatar masu da cewa matsayinsu fa, da nasu ba xaya ba Sallahu Alaihi Wasallam. Shi Annabi ne da Allah Ta’ala ke yi wa baiwa da luxufi irin wadda bai yi wa kowa ba.

4.16.2 Umurni da Fitar da Zakkar Fid-Da-Kai:

Saboda jinqayi da son alheri ga al’ummarsa, Annabi Sallahu Alaihi Wasallam ya umurci Sahabbai da fitar da Zakkar fid-da-kai, don ta zama kaffara gare su, a kan wasu ‘yan qananan abubuwa da suka iya aikatawa, irn waxanda aka hana mai ibadar Azumi ya aikata, don kada Azuminsa ya sami tasgaro.

Dan Umar Raliyallahu Anhu na cewa: “Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam ya yi umurni da fitar da sa’i xaya na dabino ko sha’iri a matsayin Zakkar fid-da-kai a kan kowane musulmi; namiji da mace, yaro da babba, xa da bawa. Ya kuma ce a bayar da ita kafin mutane su fita zuwa Sallar Idi, a ranar Sallah.”1 Haka kuma an riwaito Addullahi xan Sa’alabata Raliyallahu Anhu na cewa: “Kwana biyu ko xaya kafin ranar Sallah, Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam ya yi wa mutane huxuba yana mai cewa: “Ku bayar da sa’i xaya na alkama ko acca, ko dabino ko shari’ri a kan kowane kai, yaro da babba.” 2 Shi kuwa Abu Sa’ida Al-Khudari Raliyallahu Anhu cewa yake yi: “A zamanin Manzom Allah Sallahu Alaihi Wasallam mukan fitar da sa’i xaya ne na abin ci a matsayin Zakkar fid-da-kai.” A lokacin kuwa a cewarsa: “Abincinmu bai wuce sha’iri da zabibi da aqdu da dabino ba.”3

Shi kuwa xan Abbas Raliyallahu Anhu ga abin da ya ke cewa: “Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam ya yi umurni da fitar da Zakkar fid-da-kai don ta zama kaffara ga mai Azumi a kan wata ‘yar karauniya da yasassun maganganu, a kuma wadatar da miskinai da abin ci. Wanda duk ya fitar da ita kafin Sallar Idi a ranar Sallah, to, ta karva sunanta an kuma karva. Wanda kuwa ya bari da gangan, sai da aka sauko Idi sannan ya fitar, to ya yi sadaqa ne kawai ba Zakkar fid-da-kai ba.”4 Amma duk wanda bai san watan Sallah ya tsaya ba, sai da aka sabko daga Idi , ko kuwa yana cikin halin tafiya, ko a garin da yake zaune babu wanda ya cancanci a ba wa Zakkar, to, ya halasta gare shi ya fitar da ita duk lokacin da damar hakan ta samu, bayan qare Sallar ta idi. Allah Maxaukakin Sarki mai rahama ne da jinqayi, ba ya kuma xora wa rai abin da ba ta iyawa.”5

Bisa wannan matashiya a wannan zamani namu, duk da kwaxayin da ma’abuta addini ked a shi na aikata ayyukan alheri, bai cika mizani ba a wannan vangare na Zakkar fid-da-kai. A kan haka muke ganin yana da matuqar kyau masu da’awa su qara wayar wa da mutane kai, a kan wannan ibada da abin da ya sa aka Shar’anta ta a kansu. Wato tabbatar da ganin farin ciki ya leqa gidan kowane musulmi a safiyar ranar Sallah. Bisa wannan dalili ne kuma, da magan-ganun da ke yawan tasowa a kowace Shekara, a kan wannan ibada ta Zakkar fid-da-kai, kamar yadda suke yawan tasowa a kan adadin raka’o’in Sallar Tarawihi, muke ganin ya wajaba:
(1) A yi wa Malaman da suka halasta fitar da kuxi a matsayin Zakkar fid-da-kai, da waxanda ke amfani da wannan fatawa tasu uzuri, kuma xayan waxancan abubuwa da Sunnah ta zo da su shi ne mafifici. Amma kuma wannan ba zai kore wannan qoqari nasu ba, domin sun yi shi ne da kyakkyawar niyya, ta son tabbatar da hikimar da ke cikin wannan ibada da amfaninta.

Irin wannan banbancin fahimta da ke tsakaninmu da su, abu ne mai daxaxxen tarihi, da ba za iya magancewa ba. A kan haka muke ganin mafificin abu shi ne ko wane musulmi (xalibi) ya tsaya a kan fatawar da dalilinta ya fi qarfafa gare shi, ya kuma shirya fuskanta da sauraren qalubalen xayan vangare. Amma ya kama bakinsa kar ya ce komai. Bayan wannan kuma sai a taru gaba xaya a faxakar da jama’a cewa, wannan banbancin fihimta da suka gani a cikini wannan ibada, abu ne da ke da asali da gindin zama a Shari’a.

Yin haka zai sa mutane su qara aminci da Malamai masu qoqari a cikin addini, su kuma gane hikimomin da ke cikin kowace ibada. Ko shakka babu, hakan ya fi ci gaba da irin waxancan gardamomi marasa amfani, da ke kawai vata zukata da ayyukan bayi. A qarshe a tashi tutar babu; ba tulu ba ruwan daxi. Kamar yadda Allah Subhanahu Wa Ta’ala ya mantar da Annabi Sallahu Alaihi Wasallam takamammen daren Lailatul-Qadri, saboda jayayyar da wasu mutane biyu daga cikin musulmi suka yi a kansa.
(2) Ya fi kyau mutum ya yi qoqari ya fitar da wannan Zakka ta fid-da-kai ta hanyar amfani da kalar abinci mafi rinjaye agarin da yake zaune a ciki. Yin haka shi ne mafi zama salama, da dacewa da Sunnar Annabi Sallahu Alaihi Wasallam da haxuwar kan al’umma. Savanin fitar da kuxi, abin da suka yi savani a kai.
(3) Idan za a fitar da wannan zakka kamata ya yi a fitar da ita da nau’in abin cin da talakawa suka fi buqata, ba wanda masu fitarwar suka fi so da sha’awa ba. Dalili kuwa shi ne cewa aka yi a wadatar da talakawan a ranar idi. Duk da yake dai, kowane irin nau’i na abin ci aka fitar da shi ya yi, amma dai an fi son wanda talakawa za su yi lale marhabin da shi, ya kuma kashe masu qwandar kwaxayi da yunwa ko da a yinin ranar Sallah ne kawai. Allah shi ne mafi sani.

Haka kuma wasu na’uka na hatsi da wasu mawadata ke raba wa talakawa a wannan rana a matsayin Zakkar, ba su da wani amfani. Saboda rashin kyawonsu, qarshenta dole su sayar wa wasu yan kasuwa, su kuma su sake sayar wa wasu attajirai. Su kuma su sake raba wa wasu talakawa su, a matsayin Zakkar. Ka ga amfani ya koma ga attajiran ‘yan kasuwa ke nan, ba talakawa ba.

Ko shakka babu wannan babban kunkure ne. Dole ne, kamar yadda muka faxa a baya kaxan, idan za a fitar da wannan Zakka, a nemi hatsi mai kyawon gaske. Domin kuwa da haka ne kawai za a iya faranta wa talakawa rai a wannan rana. Kuma da mutane sun dage a kan haka, lalle da wasu hakunce-hukunce sun bayyana a kan matsalar bayar da wasu nau’o’in hatsi da abin ci. Wanda hakan za ta taimaka ga rage yawan talakawa a manyan biranen duniya. Domin kuwa matuqar ana qoqarin rage kaifin talakawa da ke damuwar masau xan qarfi, to kuwa arzikin da ke hannun mawadata ba zai wuce min sharri balle ya kai ma halaqa ba. Kamar yadda ya ke faruwa a yau a qasashen da ke gudanar da tsarin jari hujja, inda za ka taras da wasu ‘yan tsirarun mutane sun murxe dukiyar al’umma.
(4) Ya kamata kuma a fahmici cewa, ba ya halatta a xauki Zakkar kono daga wani gari ko wata qasa zuwa wasu. Lalle ne mutum ya raba ta a cikin garin da yake zaune. Abin da ke faruwa a yau na yawo da ita gari-gari, qasa-qasa, ko shakka babu kuskure ne, da ke da buqatar gyara. Domin kuwa hakan na yamutsa hazon tsarin baki xaya, wanda a qarshe haqqin ba zai isa ga masu shi na haqiqa ba, balle masu fitarwar su sami wuyan hannunsa.
(5) Abin da wasu mawadata ke yawaita yi a yau na damqa wa wasu hukumomi da ma’aikatu da qungiyoyi Zakkokinsu na fid-da-kai, don raba wa talakawa, na da buqatar gyara. Dalili kuwa shi ne waxannan mutane a haqiqa suna wakiltar masu fitar da Zakkar kawai ne ba talakawa ba. Saboda kowa suka ga dama ba wa suke yi, su kuma hana wa wanda suka ga dama, ba tare da kula da canantar na farko ko rashin ta ga mai bi masa ba. Iyakar buqatarsu ita ce a dai sauko Idi, wani abu rage na Zakkar a qasa ba. Saboda haka lalle ne irin waxannan mawadata su tabbatar da adalci da amanar duk wanda za su damqa wa iri wannan amana, tare da tabbatar da cewa zai raba ta kamar yadda Shari’a ta shata. Idan kuwa ba haka ba, to lalle da sauran rina a kaba.
4.16.4 Wakilta su ga Wasu Ayyuka.

An riwaito Abu Hurairatya Raliyallahu Anhu na cewa: “Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam ya wakilta ni, tsare wata Zakka da aka tara ta fid-da-kai. Sai wani mutum ya zo yana xiba. Ni kuwa na kame shi, na kuma nace a kan lalle sai mun gurfana da shi gaban Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam…”1

Ka ga wanan Hadisi na nuna mana yadda Annabi Sallahu Alaihi Wasallam kan rage wa kansa nauyi ta hanyar wakilta Sahabbai. Da ma kuma ai hannu xaya ba ya xaukar jinka, kamar yadda itace xaya ba zai iya karba sunan gandun daji ba. Kuma ko shakka babu sai ta irin wannan hanya ce kawai mai da’awa ke iya wanzar da wasu ayyuka da suka hau kansa. Sai dai kuma wajibi ne kafin mai da’awa ya wakilta wani daga cikin Sahabbansa ga wani aiki na da’awa, ya tabbatar da cewa ta amince masa ga wannan aiki, domin kuwa ba kowane mutum ne ake wakiltarwa ga wani aiki ba, matuqar ana so kwalliya ta biya kuxin sabulu.

Masaniyar da manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam ke da ita da halaye da xabi’un Sahahabbai, da abin da kowane xaya daga cikinsu ke iyawa, da walilta su a daidai gurabun ne, suka taimaka masa ga isar da saqon Allah. Aka wayi gari suka zama fitilu masau haske, kuma ginshiqan daular Musulunci, wanda hakan ta haskaka rayuwar 'yan Adamu a duniya baki xaya. Wannan shi ne abin da Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam ya yi ba ragi ba qari. Ya tarbiyyanci Sahabbai ne, don su zama shugabannin al’umma, ba bayi da fadawansa ba.

Amma abin mamaki a yau, za ka taras ba haka mafi yawan malamai damanyan masu wa’azinmu suke ba, tattare kuma da tutiyyar da suke yi ta zama nagartattun bayi. Sai ka taras da sun tara aiki dubu gabansu. A qarshe kuma su kasa aiwatar da xari xaya, ko su mayar da hankali ga wasu tarin ayyuka maras cikakken amfani, wanda da za su yi amfani da wannan lokaci ko kashi xaya bisa goma nasa, a kan wani aiki xaya muhimmi, ya fi. A wasu lokutan kuma ko da sun yarda su wakilta wani daga cikin Sahaban nasu ga wasu ayyuka, sai ka taras sun wakilta rubabi-rubabi gudanar da aikin ba ko alama.

Manyan Malamai da masu wa’azi a yau na da matuqar buqata fiye da kowane lokaci da irn wannan koyarwa ta Annabi Sallahu Alaihi Wasallam, wato wakiltarwa. Masamman a cikin wannan wata mai alfarma, kasancewar qofofin ayyakan alheri buxe kodayaushe. Kuma ga su nan ko’ina a wannan lokaci, ana qara fitowa da wannan buqata a fili. Amsa wannan kira kuwa zai taimaka ga samar da matasa waxanda za su maye gurbin magabata.

Koyi da wannan Sunnah ta Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam ga masu da’awa wajibi ne, domin kuwa ba a fafa gora ranar tafiya. Idan aka sa wa matasan almajirai ido ba a koya masu manyan ayyuka ba, suka samar wa kansu wasu ayyuukan na daban, to ko shakka babu idan ranar bukatar su ta kama ba za a sha da daxi ba, sai dai a yadda suka dama.

Da wanann muke roqon Ubagijinmu Allah, ya yi mana jagora, ya xora mu a kan abin da zai taimaki Musulunci da musulmi a kan wannan hanya da muke kai, ta wa’azi da karatarwa.


4.16.5 Cigaba da Aikin Qwarai:

Ci gaba da aikata nagartattun ayyuka, ba tare da la’akari da wani kevantaccen lokaci ko wuri ba, na sa musulmi ya dace da yardarm Allah Subhanahu Wa Ta’ala. Kan haka ne Annabi Sallahu Alaihi Wasallam cikin jinqayi da rahama irin tasa yake kwaxaitar da Sahabbai, a kan ci gaba da yin Azumi ko bayan wucewar Ramala, wato Azumin nafila inda yake cewa: “Duk wanda ya azumci Ramalana ya kuma rufa masa baya da Azumin kwana shida a cikin watan Shauwal, to kamar ya azumci zamani ne gaba xaya.”1 Ba lalle ne ayyukan nagarta da xa’a su kasance masu yawa ba, a’a, albarkar abu ta fi yawansa. Kuma mafi soyuwar aiki a wurin Allah Subhanahu Wa Ta’ala shi ne wanda kyakkyawan aiki da mummuna dukan su, qorai ne da ke biye da ‘yan‘uwansu koyaushe. Saboda haka ne Annabi Sallahu Alaihi Wasallam bai tava fara aikin alheri ya daina ba,2 sai daxi.3

Babu wani dalili da zai hana mai koyi da Sunnar Annabi Sallahu Alaihi Wasallam ci gaba da ayyukan alheri, matuqar dai da gaske yake yi. Karewar watan Ramalana ba hujja ba ne, domin kuwa babu watan da Allah ba ya nan a cinkinsa balle. Yau da gobe kuma ba ta bar komai ba, kullum kwanki sai baya suke yi, samun shiga Aljanna kuwa sai an yi da gaske domin ba ta rago ba ce. Sai an so Allah so na haqiqa an kuma zare dantse an yi auyuka na qwarai ba dare ba rana, sannan ne ake iya samun lasisin shiga Aljanna.

Tabbatattar magana ce cewa, Sunnah ta tanadi mutum ya yawaita ibada a cikin watan Ramalana fiye da kowane lokaci, kamar yadda ya zo a cikin Hadisin xan Abbas Raliyallahu Anhu cewa: “Mazon Allah Sallahu Alaihi Wasallam ya fi kowa kyauta a cikin al’umma musamman idan watan Ralamana ya kama, abin babu kama hannun yaro.”4 A wani Hadisi kuma Nana Aisha Raliyallahu Anha na cewa: “Idan kwanaki goba na qarshen watan Ramalana suka kama, Manzon Allah Sallahu Alaihi Wasallam kan qara qaimin ibada fiye da kowane lokaci.”1 Amma idan aka dubi waxannan nassosa da idon basira, to za a fahimci cewa, bayanin da suke yi na qaimin da Annabi Sallahu Alaihi Wasallam ke qarawa a kan ibada da ayyukan alheri, a cikin wannan wata na Ramalana na tafiya ne kafaxa-da-kafaxa, da tabbatar wa mai karatu da cewa ba lokacin watan Azumin kawai yake waxannan ayyukan alheri ba, idan kuma ya wuce shi ke nan.

Wannan magana na tabbata ne, idan aka yi la’akari da lafazin da ke cikin nassosan na qara qaimi. Ashe da ma can da akwai qaimin, qara shi ne kawai yake yi a wannan lokaci Sallahu Alaihi Wasallam. To ko banza, a tsarin Musulunci watan Ramalana wata ne na xaukar haramin gudanar da rayuwa a cikin sauran kwanaki da watannin shekara. Wanda haramarsa ta fi kyau da qarfafa, to zai kammala shekararsa da qarfi da kyakkyawan sakamako. Ashe kuwa mai hankili duk, zai qara qaimi a cikinsa. Kuma a fili take cewa sauran kwanakin shekarar mutum ba za su yi kyau ba, matuqar bai sha daurin sanin girman Allah da qiyaye dokokinsa ta hanyar yawita bauta da ayyukan alheri a lokacin Azumin Ramalana ba. Sai da haka ne zai gane duniya ba bakin komai take ba. Kuma abin da Allah ya tanadar wa bayinsa muminai na mamaki a cikin Aljanna, ya fi, nesa ba kusa ba.2 Kamar yadda kuma abin da ya tanada a Wuta na azaba don kangararru daga cikin bayinsa ya fi qarfin duk wani nau’i na azaba da ke bisa doron qasa.

To kuma inda ma gizo ke saqar shi ne ba kawai mutum ya yi ta ibada a cikin watan Ralamana da bayansa ba kawai. A’a ba zai sami moriyarta ba, sai ta ratsa jini da tsokarsa, ta yadda ba yadda za a yi ya sami kwanciyar hankali da natsuwa idan ba ita ya yi ba, a matsayinta na abin da ya fi soyuwa gare shi. Haka Annabi Sallahu Alaihi Wasallam ya xauki ibada. Dubi abin da yake ce wa Bilalu game da Sallah, Sallahu Alaihi Wasallam : “Ya kai Bilalu ta shi ka kira Sallah, ko muna samu hankalinmu ya kwanta.3 Da kuma cewar da ya yi: “Allah ya sa mani so da qaunar yin Sallah fiye da yadda ido ke son ya yi tozali da abin da yake so.4 Kai qarewa da qarau, wani dare yana xakin Aisha Raliyallahu Anha sai yake ce mata: “Ya ke Aisha xan yi haquri ina son in xan yi ibada zuwa ga Ubangijina.” Aisha Raliyallahu Anha ta ce: “Sai na ce masa a gaskiya ina da buqata da kai. Amma kuma duk da haka, ba ni son abin da zai vata maka rai.” Ina qare faxar haka inji ta, sai ya tashi ya yi arwalla ya kama Sallah,” A qarshe kuma yanayin Sallar kamar yadda ta bayyana, sai wanda ya gani saboda tsananin kukan da ya dinga a ciki, da qasqastar da kai da fadanci a wurin Allah5 (Koma fasali na Biyu)

Haka ake so Sallar kowane musulmi ta kasance. Savanin yadda mafi yawan mutane ke yi yanzu, wato yin ibada cikin kasala da nauyin jiki, ana kuma gaggawa irin ta mai son ya jefar da xan magawaro don ya huta da quda. Irin wannan xabi’a kuwa na sa musulmi, a cikin halin kaxaita ko cikin taro, yin babbar hasarar da Allah Subhanahun Wa Ta’ala ne kawai ya san iyakarta, na vata lokaci matuqa ba tare da sun damu ba, ana wasu abubuwa marasa amfanin yau bare na gobe. Alhali kuwa kamata ya yi, ya tanadi wani abu na nafila, wanda za su iya cike wani givi da shi gobe qiyama komai kuwa qanqantar azaba, koko ya xaga darajarsu zuwa wani mataki na gaba.

Yau, da wannan al’umma za ta yi binciken qwaqwaf, ta tantance irin lokacin da qarfi da damar da xaixaikunta ke vatawa a iska, da ta yi kukan uwar Musa. A yi amfani da ita a fagen da’awa da sauran ayyukkan alheri na ibada irin waxanda ake gudanrawa lokaci-lokaci, a matakin xaixaiku da jama’a da an yi matuqar mamakin irin ci gaban da za a samu. Ko banza ga shi watan Ramalana da lokuta masu kama da shi, lokaci ne da kowane musulmi ya sakankance da cewa, zai iya yawaita ayyukan alheri a cikinsa ninkin-ba-ninkin. Domin akwai damar yin haka, matuqar ya sa kansa ya kuma nemi taimako da gudunmawar Allah Maxaukakin Sarki.

Wannan wata na Ramalana wani ma’auni ne da musulmi ke iya auna kansa da shi, ya gane abin da yake iyawa na qwazo a fagen ibada ko ba a cikin watan ba, tunda, ya tava yi, gain kuwa ya kori ji. Haka kuma ma’auni ne shi na tabbatar masa da cewa babu wani shexanin mutum ko aljani, da zai iya rinjayarsa, ko Azumi ya wuce, tunda da shi, ya yi galaba a kansa wani lokaci domin qarfin imanin da ya taimake shi a kansu. A wancan lokaci abu ne da ke tare da shi kodayaushe. Haka kuma gidan Aljanna da na Wuta suna nan suna jiran ma’abutansu, shi kuma Allah Ubangijin bayi Rayyaye ne ba ya kwana ba ya angaje.

Da wannan muke kira ga ‘yan’uwa musulmi da cewa kar mu yi sake, mu yunqura tun watan Ramalana bai bi rana ba. Aka kwance tare da saya na Aljanna Mu yi qoqari kafin haka ta faru mu kama lafiyayyar hanya wadda za mu sadu da watan Azumin baxi muna a cike da qoshin lafiya da kwaciyar hankali. Sannan mu sake xaukar sabon harami da guzuri, muna Allah Maxakakin sarki mai kowa mai komai.

Wani abu kuma da nake jin ya kamata in ja hankalinmu zuwa gare shi kafin in xiga aya shi ne, a zahiri cewar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wa Sallam ya yi: “Duk wanda ya azumci watan Ramalana sannan ya rufa masa baya da Azumin kwanaki shida a cikin shauwal……” Wannan magana na nufin wanda bai sha Azumi ko xaya ba na Ramalana. Amma idan akwai wani abu a kansa na bashi, to lalle ne sai ya biya shi kafin wannan. Ya samu kuma ya xan sa rana bayan rankon, duk da yake an fi son a yi su nan take. Domin azumtar waxannan kwanuka a ranar talata da alhamis da ayyumulbil ya fi lada bisa ga yin su a cikin wasu kwanaki. Allah shi ne mafi sani.

Allah ka sa mu dace, ka cusa mana shiriya, ka yi mana rahama, ka kuma yi mana toliya da ihsaninka. Ya mafi girman masu girma, mafi alheririn masu jinqayi.





Yüklə 0,65 Mb.

Dostları ilə paylaş:
1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12




Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©muhaz.org 2024
rəhbərliyinə müraciət

gir | qeydiyyatdan keç
    Ana səhifə


yükləyin